Yan Sanda Sun Cafke Wani da Niyyar Kashe Almajiri Don Daukar Fansa Kan Malaminsu

Yan Sanda Sun Cafke Wani da Niyyar Kashe Almajiri Don Daukar Fansa Kan Malaminsu

  • Wani mutum mai suna Dayyabu Yusuf ya shiga hannu bayan kama shi da zargin shirin kashe almajiri a jihar Bauchi
  • Yusuf ya kuduri aniyar ce don daukar fansa bayan malamin yaron ya lalata shirin aurensa a karamar hukumar Jama’are
  • Ya ce bayan ya dauki yaron zuwa dajin don aiwatar da abin da ya yi niyya sai ya gagara saboda babu laifin yaron

Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta cfke wani mutum kan zargin kokarin hallaka wani almajiri a jihar.

Ana zargin mutumin mai suna Dayyabu Yusuf dan shekaru 39 da nufin daukar fansa kan almajirin bayan malaminsa ya lalata shirin aurensa a karamar hukumar Jama’are.

An cafke wani kan yunkurin kashe almajiri don daukar fansa a jihar Bauchi.
Yan Sanda Sun Cafke Wani da Yunkurin Kashe Almajiri. Hoto: Bala Mohammed.
Asali: UGC

Meye wanda ake zargi da kisan almajirin ke cewa?

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Auwal Musa shi ya gurfanar da Yusuf tare da wasu masu laifi daban-daban a jihar, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf ya shaidawa ‘yan jaridu cewa tun bayan gabatar da malamin almajirin a cikin lamarin aurenshi ya fara samun matsala shi yasa ya dauki wannan mataki na daukar fansa.

Ya ce:

“Komai na tafiya yadda ya kamata a baya, daga shigan malamin komai ya koma baya, ya fara bata min suna a wurin mahafin yarinyar har auren ya lalace.
“Mahaifiyar yarinyar ta kiran ta ce na yi hankali da malamin kan shirin aure da na ke yi.
“Bayan samun wannan bayani ban samu natsuwa ba har zuwa lokacin da mahaifin yarinyar ya ce na dakata da neman auren.”

Yusuf ya ce ya dauki almajirin zuwa dajin don hallaka shi saboda ya dauki fansa kan abin da malamin ya yi don ya ji zafi shi ma.

Ya kara da cewa bayan ya isa dajin ne ya gagara aiwatar da abin da ya yi niyya saboda ba shi da laifi a ciki.

Kara karanta wannan

Wayyo ‘Yan Bindiga Za Su Karasa Mu – ‘Dan Majalisa Ya Kai Kuka Wajen Gwamnati

Meye martanin 'yan sanda kan kisan almajirin a Bauchi?

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa a rahoton da su ka samu Yusuf na da matsala da Mallam Faisal kan lamarin aure inda ya ke son daukar fansa.

Ya ce Yusuf ya yaudari Faruku Faisal mai shekaru 14 daga tsangayar Mallam Faisal zuwa daji don kashe shi ba don tsafi ya yi niyyar hakan ba.

Har ila yau, 'yan sanda kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito sun kama wata mata mai suna Khadija Adamu kan zargin kashe 'yar kishiyarta a jihar Bauchi a farkon wannan wata.

'Yan bindiga sun hallaka 'yan sa kai a Bauchi

A wani labarin, 'yan bindiga sun hallaka 'yan sa kai har mutane guda tara a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeirya.

Wannan na zuwa bayan 'yan sa kai din sun addabi 'yan bindigan a kwanakin baya tare da musu barna mai tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel