Wazirin Fika, Adamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 90

Wazirin Fika, Adamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 90

  • Ana cikin makoki bayan rasuwar Shahararren dan siyasa kuma ma'aikacin gwamnati, Alhaji Adamu Fika
  • Marigayin ya rasu ne a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba yayin da ya ke cikin jirgi a kan hanyar dawo wa Najeriya
  • Fika ya rike mukamai da dama da su ka hada Sakataren Gwamnatin Tarayya da shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya da sauransu

Jihar Kaduna - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Adamu Fika ya rasu ya na da shekaru 90 a duniya.

Marigayin wanda shi ne Wazirin Fika ya rasu a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba a cikin jirgi yayin da ake dawo da shi da daga Ingila.

Wazirin Fika, Adamu ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya
Allah ya karbi rayuwar Wazirin Fika, Alhaji Adamu Fika. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin, Wazirin Fika ya rasu?

Danburan Fika, Alhaji Idris Adama Kukuri shi ya tabbatar wa Daily Trust labarin mutuwar a wata ganawa ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kunno a APC, Ana Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisar Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa yanzu ba a sanar da lokacin jana'izar ba inda majiyarmu ta ce sai an tuntubi Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali.

Majiyar ta ce jirgin da ya dauko marigayin ya sauka a Kaduna inda ake tunanin binne shi a can ko kuma komawa da shi Fika da ke jihar Yobe.

Wasu mukamin marigayin, Wazirin Fika ya rike?

Fika, kafin rasuwarshi ya rike mukamai da dama a gwamnati da samun lambar yabo masu tarin gaske, Leadership ta tattaro.

Fika kafin rasuwarshi, ya rike mukamin sakataren din-din-din a ma'aikatun Gwamnatin Tarayya da dama da su ka hada da ma'aikatar Kasuwanci da Sadarwa da kuma ta harkokin cikin gida.

Za a yi sallar jana'izarsa a masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna a yau Laraba 25 ga watan Oktoba dai misalin karfe 4:00 na yamma.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari Ya Yi Ya Jawo darajar Naira ta ke Karyewa a Yau – Sanatan PDP

Sabon kwamishina a jihar Borno ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, sabon kwamishina a jihar Borno, injiniya Ibrahim Idris Garba ya riga mu gidan gaskiya a gidansa da ke Maiduguri babban birnin jihar.

Marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Asabar 21 ga watan Oktoba a rukunin gidajen 777 a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Rasuwar tashi na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Babagana Zulum ya nada shi kwamishinan ayyuka da gyararraki da sake matsuguni a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel