Sabon Kwamishina a Jihar Borno Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Asabar

Sabon Kwamishina a Jihar Borno Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Asabar

  • Ana cikin jimami yayin da sabon kwamishina a rasa rayuwarsa a jihar Borno da safiyar yau Asabar
  • Marigayin mai suna Injiniya Ibrahim Garba ya rasa ransa ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri, UMTH
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa guba ne sanadin mutuwar sabon kwamishinan na jihar Borno

Jihar Borno - Allah ya yi wa sabon kwamishinan gyara da sake matsuguni a jihar Borno rasuwa da safiyar yau Asabar.

Marigayin Injiniya Ibrahim Idris Garba ya rasu ne a gidansa da ke rukunin gidajen 777 a Maiduguri, babban birnin jihar, Legit ta tattaro.

Sabon kwamishina a Borno ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu da safiyar yau Asabar. Hoto: Injiniya Ibrahim Idris/Facebook.
Asali: Twitter

Menene sanadin mutuwar kwamishinan a Borno?

Ibrahim wanda ya samu mukamin kwamishinan a kwanakin nan ya rasu a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Fara Bincike Bayan Sabon Kwamishina Ya Yi Mutuwar Bazata

ZagazOlaMakama ya tabbatar da mutuwar kwamishinan a shafin Twitter inda ya ce guba ne sanadin mutuwarshi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu da safiyar yau Asabar 21 ga watan Oktoba a Maiduguri.

Sanarwar ZagazOlaMakama ta ce:

"An yi babban rashi yayin da sabon kwamishinan ayyuka, gyara da sake matsuguni a jihar Borno ya rasu.
"Ya rasu a gidansa da ke rukunin gidajen 777 da ke Maiduguri, an sanar da mutuwarshi a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri.
"Ana kyautata zaton guba ce ta yi ajalinshi."

Wane mukami marigayin ke rike da shi a Borno?

Sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne sanadiyyar ciwon zuciya da yake fama da shi.

Marigayin bayan mukamin kwamishina, ya kasance hadimin Gwamna Babagana Zulum a bangaren kula da ayyuka.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba mu samu martan daga gwamnatin jihar ba kan wannan babban rashi na sabon kwamishinan a jihar.

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Rasa Ranta Bayan 'Yan Ta'adda Sun Yi Mata Yankan Rago a Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

'Yan Kalare sun yi wa wata mata yankan rago a Gombe

A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan Kalare ne sun yi ajalin wata dattijuwa mai shekaru 58 a jihar Gombe.

Marigayiyar mai suna Aishatu Abdullahi da aka fi sani da 'Adda Damori' ta rasa ranta bayan an yi mata yankan rago a gidanta.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mahid Mu'azu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun fara gudanar da bincike kan kisan gillar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel