Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 7 da Dukiyar Miliyan 25 a Babbar Kasuwa, Gwamna Ya Yi Martani

Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 7 da Dukiyar Miliyan 25 a Babbar Kasuwa, Gwamna Ya Yi Martani

  • An tafka asara bayan mummunar gobara ta cinye wani bangaren wata kasuwa a Calabar babban birnin jihar Kuros Riba
  • Lamarin ya faru ne a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba inda mutane ke zargin yawan wayoyin wutar lantarki a sama ne dalili
  • Wani mai shago a yankin, Uchenna Orji ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an yi asarar fiye da naira miliyan 25 sanadin gobarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kuros Riba – Iftila’in gobara ta cinye wani bangaren babbar kasuwar Watt da ke tsakiyar birnin Calabar a cikin jihar Kuros Riba.

‘Yan kasuwar sun zargi wayoyin wuta da ke rataye a mafi yawan fola-folai da ke tsagaye da kasuwar ne dalilin jawo gabarar.

Gobara ta lakume dukiyar miliyan 25 a Calabar
Gobara ta yi sanadin asarar miliyoyi a Calabar. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Yaushe gobarar ta afku a jihar Kuros Riba?

Lamarin ya faru ne a yau Alhamis 26 ga watan Oktoba inda aka yi asarar fiye da naira miliyan 25 sanadiyyar gobarar a yankin.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Sha Kaye a Kotun Ƙoli, Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani daga cikin ‘yan kasuwar, Orji Uchenna ya bayyana wa Daily Trust cewa iftila’in ya yi sanadin asarar nailra miliyan 25 na jama’a.

Ya ce shagona akalla bakwai su ka kone kurmus a kan hanyar Hewett da ke manne da kasuwar a Calabar, Trust Radio ta tattaro.

Meye martanin Gwamna kan wannan gobara a Kuros Riba?

Ya kara da cewa lokacin da gobarar ta fara, jami’an kashe gobara sun iso wurin da gaggawa amma abin takaici babu ruwa a tare da su.

Jami’an sun yi alkawarin nemo ruwan don dawo wa tare da ba da tasu gudunmawa don dakile wutar amma ba su dawo ba.

Hadimin gwamna jihar, Barista Ekponyong Akiba wanda ke wurin da lamarin ya faru ya jajantawa wadanda iftila’in ya shafa.

Ya shawarci shugabanin kasuwar da su dauki sunayen wadanda abin ya shafa don saukakawa Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta NEMA don rage wa mutane radadin asara.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Tsaro, Sun Buɗe Wa Motocin Matafiya Wuta a Arewa

Gobara ta jawo asara a babbar masana'anta a Legas

A wani labarin, mummunar gobara ta tashi a wata masana'antar sarrafa robobi da ke jihar Legas.

Lamarin ya faru ne a masana'antar da ke yankin Mushin da ke jihar inda jami'an kashe gobara ke kokarin kashe wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel