Kotu Ta Yankewa Likita Daurin Rai Da Rai Saboda Yi Wa Yar’uwar Matarsa Fyade

Kotu Ta Yankewa Likita Daurin Rai Da Rai Saboda Yi Wa Yar’uwar Matarsa Fyade

  • Kotu ta yankewa Dr Femi Olaleye daurin rai da rai a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, bayan samunsa da laifin aikata fyade
  • Dr Olaleye ya kasance shugaban Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Optimal wanda aka zarga da yi wa yar'uwar matarsa mai shekaru 15 fyade
  • A wani hukunci a ranar Talata, kotun ta riki cewa lallai likitan ya haikewa yarinyar

Ikeja, jihar Lagas - Wani kotun Ikeja ya yankewa shugaban Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Optimal, Dr Olufemi Olaleye, hukunci a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba kan yi wa yar'uwar matarsa fyade.

Kotu ta daurewa likita daurin rai da rai
Kotu Ta Yankewa Likita Daurin Rai Da Rai Saboda Yi Wa Yar’uwar Matarsa Fyade Hoto: @CancerOptimal
Asali: Twitter

Da yake zartar da hukunci, Maishari'a Rahman Oshodi ya bayyana cewa masu shigar da kara sun gamsar da kotun da hujjojin da suka tabbatar da cewa Olaleye ya aikata laifin, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Daga Rantsar da Shi, An Fara Kutun-Kutun a Kotu Domin Tsige Sabon Shugaban EFCC

Alkalin ya zartar da cewar hukuncin da aka gabatar a kan babban likitan na da karfi kuma ya yi daidai da abun da wacce aka yi wa aika-aikan ta bayyana, PM News ta rahoto.

Hakan na zuwa ne bayan Dr Olaleye ya jaddada cewa zarge-zargen da ake yi masa karya ne da kuma mugun nufi da kuma kokarin bata suna. Daga baya likitan ya fuskanci tuhume-tuhume biyu na zargin lalata da cin zarafi ta hanyar shigar yarinyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yankewa malamar musulunci daurin rai da rai

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa kasar China ta yanke hukunci kan malamar addinin Musulunci a Uyghur bisa zargin barazana da tsorata kasa. Rahila Davut mai shekaru 57 wacce ke koyarwa a jami’ar Xinjiang, an yanke mata hukuncin daurin rai a rai.

Kara karanta wannan

Sojojin Sun Share Hawayen 'Yan Arewa, Sun Sheke Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda

Ana zargin kasar China da kamawa tare da daure mutanen Uyghur tare da muzanta musu wurin dakile haihuwa da kuma yada al’adunsu.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na zargin wasu masu rike da mukaman gwamnati da kisan kiyashi kan mutanen Uyghur.

APC ta dakatar da jigonta Kan Zargin Fyade

A gefe guda, shugabannin jam’iyyar APC na reshen jihar Jigawa sun dakatar da shugabansu na karamar hukumar Roni, Saleh Idris.

Ana zargin Alhaji Saleh Idris ne da zargin yi wa karamar yarinya mai shekara 14 fyade, wanda hakan ya kai ga samun juna biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel