Tsohon Hadimin Shehu Buba Ya Tashi da Babbar Sarauta a Daular Usmaniyya a Sokoto

Tsohon Hadimin Shehu Buba Ya Tashi da Babbar Sarauta a Daular Usmaniyya a Sokoto

  • Tsohon hadimin Sanata Shehu Buba, Abba Aliyu Tilde, ya samu sarautar gargajiya a Daular Usmaniyya da ke Sokoto
  • Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya nada Sheikh Mansur Sokoto a matsayin Ɗan Masanin Daular Usmaniyya
  • Abokin Tilde, Nuruddeen Haske, ya taya shi murnar samun sarautar, yana mai bayyana nadin a matsayin babban abin alfahari da girmamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Tsohon hadimin Sanata Shehu Buba, Abba Aliyu Tilde ya samu sarautar gargajiya a Daular Usmaniyya a Sokoto.

A yau ne Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi nade-nade a masaurautar da ke Sokoto.

Aliyu Tilde ya zama wazirin Ɗan Masanin Daular Usmaniyya
Abba Aliyu Tilde, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III da Sheikh Mansur Sokoto. Hoto: Abba Aliyu Tilde, Sheikh Mansur Sokoto.
Source: Facebook

Abokin Tilde da ake kira Nurudden Yakubu Hakse shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Lahadi 1 ga Nuwambar 2026.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya naɗa ƴaƴansa, babban malamin Musulunci sarauta a Sokoto

Nade-naden aka yi a fadar Sarkin Musulmi

An nada Sheikh Mansur Sokoto a matsayin Ɗan Masanin Daular Usmaniyya yayin da Tilde ya zama wazirinsa.

Sarkin Musulmi ya nasa wasu manyan mutane sarauta a yau tare da wasu daga cikin ƴaƴansa biyu da kuma wasu manyan mutane har da Sheikh Mansur Sokoto.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ce ya yi nadin ne duba da gudunmawar da mutanen ke ba al'umma ba tare da nuna wani son kai ba.

An naɗa ’ya’yansa biyu, Abubakar Sadiq Abubakar da Shehu Usman Abubakar, sarautun Sarkin Dawaki Tsakar Gida da Fagachin Sokoto, a wani bikin musamman ranar Lahadi.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da fitaccen mai taimakon jama’a kuma malamin addinin Musulunci, Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya, a matsayin Dallatun Sokoto, da Farfesa Mansur Ibrahim a matsayin Dan Masanin Sokoto.

Tilde ya samu babbar sarauta a fadar Sarkin Musulmi
Sabon Wazirin Ɗan Masanin Daular Usmaniyya a Najeriya. Hoto: Nuruddeen Yakubu Haske.
Source: Facebook

Aliyu Tilde ya zama wazirin Ɗan Masani

Abba Aliyu Tilde ya zama wazirin Dan Masanin Daular Usmaniyya wanda aka tabbatar a yau Lahadi 1 ga watan Nuwambar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Basarake kuma babban malamin addini ya yi bankwana da duniya

Nuruddeen Haske ya bayyana farin cikinsa da samun sarautar da abokinsu ya yi da ya ce abin alfahari ne.

Ya bayyana cewa wannan nadi da aka masa ya nuna girmamawa da kuma daraja da Tilde ke da shi da ya cancanci yabo da kuma taya shi murna.

Nuruddeen Haske ya ce:

"Wannan babban matsayi ne na girmamawa da ke nuna daraja da karramawa, muna taya shi murnar wannan naɗi, tare da addu’ar Allah Ya sanya wannan matsayi ya zama sanadin ƙarin alheri, ɗaukaka da hidima ga al’umma.
"Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da ke tattare da wannan matsayi cikin adalci, hikima da nasara. Amin."

Sultan ya magantu kan salon shugabanci a Najeriya

An ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce shugabannin Musulmi za su ja hankalin masu mulki kan wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Ya bukaci shugabannin siyasa da su dauki matakan inganta rayuwar talakawa, yayin da tsadar abinci, sufuri da man fetur ke kara nauyi ga jama’a

Sultan ya kuma gargadi matasa kan bari a yi amfani da su wajen ta’addanci, fashi da makami ko rikicin siyasa domin biyan bukatun wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.