Abun Bakin Ciki
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya sallami dukkan shugabannin kananan hukumomi 21 da ke jihar inda ya ce wa'adinsu ya kare a kan madafun iko.
An shiga jimami bayan rasuwar fitaccen malami a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno, Farfesa Mustapha Kokari a jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan fama da jinya.
Rundunar yan sanda a jihar a Lagos ta tabbatar da mutuwar wani dattijo mai shekaru 50 a jihar da aka samu gawarsa bayan yaje kallon kwallo a birnin Ikeja.
Tsohon Janar na sojoji, Garba Duba wanda ya fafata a juyin mulkin shekarar 1966, ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a 18 ga watan Mayu a birnin Abuja.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan zargin batar da mahaifa da kuma cibiyar jariri a jihar bayan haihuwarsa.
Sanata Michael Onunkun wanda ya wakilci Ondo ta Yamma a jamhuriya ta biyu a Najeriya, ya rasu yana da shekaru 98 a duniya a jiya Laraba 15 ga watan Mayu.
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana kujerar marigayi Hon. Isa Dogonyaro babu kowa bayan ya rasu a ranar Juma'a da ta gabata a birnin Abuja.
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo bayan ya sha fama da jinya a yau Laraba.
'Yan sanda sun tabbatar da cewa matashin da ya babbaka masallata a kauyen Gezawa ya yi amfani da bam wajen aikata ta'adin. Amma an gano ba harin ta'addanci ba ne.
Abun Bakin Ciki
Samu kari