'Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Fadar Sarki da Karfi, Sun Tafi da Basarake

'Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Fadar Sarki da Karfi, Sun Tafi da Basarake

  • Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da fitaccen basarake, Ogwong A Abang a jihar Akwa Ibom bayan kutsawa cikin fadarsa
  • Lamarin ya faru ne a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu inda suka yi ta harbe-harbe kafin sace basaraken a fadarsa
  • Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, ASP Timfon John ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi 19 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Ƴan bindiga sun sace fitaccen basarake a jihar Akwa Ibom, Ogwong A Abang.

An yi garkuwa da basaraken ne a fadarsa da ke Ebughu a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake a Najeriya ya kwanta dama, gwamna ya nuna alhini

Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a cikin fadarsa
'Yan Bindiga sace basarake, Ogwong Abang a jihar Akwa Ibom. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Martanin ƴan sanda kan sace basaraken

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar, ASP Timfon John ita ta tabbatar da haka a yau Lahadi 19 ga watan Mayu, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Timfon ta ce rundunar ta na iya bakin kokarinta domin tabbatar da ganin an ceto basaraken, cewar rahoton Punch.

"Mun samu rahoton sace basaraken, kuma rundunarmu tana dukkan mai yiwuwa wurin tabbatar da ceto basaraken daga hannun ƴan bindiga."

- Timfon John

Miyagu sun lakadawa ƴan sanda duka

Har ila yau, an shiga wani irin yanayi bayan wasu bata gari sun lakadawa jami'an 'yan sanda duka a jihar Akwa Ibom.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan sandan ke neman wani shugaban kungiyar asiri ruwa a jallo mai suna Udo a karamar hukumar Abak ta jihar.

Kara karanta wannan

Congo: An shiga fargaba yayin da aka yi yunkurin juyin mulki, an yaɗa bidiyon

Jami’an da suka je kama Udo sunyi amfani ne motar gida inda suka yi nasarar kama shi suna kan hanyarsu ta komawa, sai motarsu ta samu matsala.

Babban basarake ya rasu a Osun

A wani labarin, An shiga cikin wani irin yanayi bayan rasuwar fitaccen basaraken gargajiya a jihar Osun.

Marigayi Oba Aderemi Adedapo ya rasu ne a yau Asabar 18 ga watan Mayu a asibitin koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Oba Adedapo shi ke saraurar yankin Ido-Osun da ke karamar hukumar Egbedore a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel