Fitaccen Basarake a Najeriya Ya Kwanta Dama, Gwamna Ya Nuna Alhini

Fitaccen Basarake a Najeriya Ya Kwanta Dama, Gwamna Ya Nuna Alhini

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya nuna alhini kan rasuwar Basarake a jihar, Oba Aderemi Adedapo
  • Marigayin wanda ke sarautar Ido-Osun ya rasu ne a jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan fama da jinya
  • Kakakin gwamnan, Olawale Rasheed shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi 19 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - An shiga cikin wani irin yanayi bayan rasuwar fitaccen basaraken gargajiya a jihar Osun.

Marigayi Oba Aderemi Adedapo ya rasu ne a yau Asabar 18 ga watan Mayu a asibitin koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife.

Kara karanta wannan

NDLEA ta fara farautar miji da mata kan safarar hodar iblis tsakanin Indiya da Najeriya

Babban basarake ya mutu yayin da gwamna ya tura sakon jaje
Basarake, Oba Aderemi Adedapo ya rasu a jihar Osun. Hoto: Osun State Government.
Asali: Facebook

Wace masarauta marigayin ke jagoranta?

Oba Adedapo shi ke saraurar yankin Ido-Osun da ke karamar hukumar Egbedore a jihar, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa inda suka ce ya fara jinya ne a makon da ya gabata.

Sanarwar ta ce an dauke shi asibiti mai zaman kansa kafin daga bisani a mayar da shi asibitin koyarwa na Jami'ar jihar Osun.

Majiyar ta ce daga bisani ya yi bankwana da duniya a asibitin koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo (OAUTHC) bayan mayar da shi can.

Gwamna ya nuna alhini kan rasuwar basaraken

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya nuna alhini kan mutawar basaraken inda ya ce abin takaici ne.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Olawale Rasheed ya fitar a yau Lahadi 19 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Fitaccen Farfesa ya riga mu gidan gaskiya a Jami'ar Maiduguri

"Tabbas an tafka babban rashi, ina tura sakon jaje ga al'ummar Ido-Osun kan wannan rashi na mutumin kirki, Adedapo."
"Yayin da muke jimamin rashin Adedapo, kada mu manta da irin ayyukan kawo ci gaba da bunkasa al'ummar yankinsa da ya yi."

- Olawale Fashewa

Farfesa Kokari ya rasu a Maiduguri

Kun ji cewa fitaccen Farfesa a Jami'ar Tarayya da ke Maiduguri a jihar Borno ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin Farfesa Mustapha Kokari ya rasu ne a jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan ya sha fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel