Abun Bakin Ciki
An shiga jimami bayan rasuwar mawaki, Godwin Opara ya na da shekaru 77 a duniya, marigayin da aka fi sani da Kabaka ya rasu ne a yau Juma'a 22 ga watan Maris.
Wasu fusatattun matasa sun lakada wa wani da ake zargin barawon babur dukan tsiya har lahira a garin Magama-Gumau da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
Hukumar EFCC ta sake bankado da maganar karkatar da kudin makamai da ake zargin tsohon shugaban PDP, halliru Bello a mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Mahara sun yi ajalin Dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki kafin daga bisani suka hallaka shi.
Mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwa da ke jihar Sokoto inda ta kone kadarorin miliyoyi wanda har zuwa yanzu ba a tantance asarar da aka yi ba.
'Yan majalisa takwas da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da su sun ce 'yan daba na farautar rayuwarsu saboda sun fallasa ta'azzarar tsaro a jihar.
Yayin da ake jimamin kisan sojoji akalla 16 a jihar Delta, Gwamna Sherrif Oborevwore ya yi Allah wadai da harin inda ya sha alwashin daukar mummunan mataki.
Yayin aka hallaka sojoji 16 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ana zargin wasu sojoji sun kona kauyen kurmus da safiyar yau.
Hukumar Kwastam a tsibirin Tin-Can da ke jihar Legas ta yi nasarar dakile kokarin shigo da muggan makamai da miyagun kwayoyi Najeriya a yau Juma'a.
Abun Bakin Ciki
Samu kari