“An Yi Amfani da Bam”: Mutum 1 Ya Mutu da Aka Bankawa Masallata Wuta a Kano

“An Yi Amfani da Bam”: Mutum 1 Ya Mutu da Aka Bankawa Masallata Wuta a Kano

  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa an yi amfani da bam na hadin gida wajen banka wuta a wani masallaci da ke jihar Kano
  • Rundunar ta kuma ce daya daga cikin mutane 24 da abin ya rutsa da su ya mutu yayin da sauran ke kwance a asibiti
  • Yayin da ta ke nesanta wannan iftila'in da harin ta'addanci, rundundar ta gano cewa fadan rabon gado ne ya jawo banka wutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Daya daga cikin masallatan da aka banka wa wuta a masallacin da ke unguwar Laraba Abasawa a karamar hukumar Gezawa a Kano ya rasu.

Mutum daya ya mutu sakamakon wutar da aka bankawa masallata a Kano
'Yan sanda sun gano an yi amfani da bam wajen kona masallata a jihar Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

AIG Umar Mamman Sanda ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa asibitin Murtala Muhammad dake Kano, inda ake kula da wadanda suka jikkata.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kone masallata su na tsakar sallar asubahi a Kano

"Ba harin ta'addanci ba ne" - AIG Sanda

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin da ya faru ba shi da alaka da duk wani aiki na ta’addanci, mun gano fada ne da ya samo asali daga rabon gado.
“An ce wanda ake zargin bai gamsu da rabon ba dalilin da ya sa shi ya aikata hakan. Yanzu dai yana hannu, muna yi masa tambayoyi."

"An yi amfani da bam" - AIG Sanda

Daga cikin mutane 24 da aka kwantar da su, AIG Umar Sanda ya ce daya ya mutu, inda ya bayyana cewa wanda ya aikata laifin ya yi amfani da bam na hadin gida.

Da wannan ne ya yi kira ga al'uma da a kwantar da hankula domin jami’an tsaro sun dauki matakan da ya dace.

AIG Umar Sanda ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa domin bayar da kulawar jinya ga wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

An kona masallata a Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani mutum wanda ba a bayyana ko wanene ba ya banka wa wani masallaci wuta yayin da ake sallar Asubah a garin Laraba Abasawa a karamar hukumar Gezawa a Kano.

A yayin da aka ba da rahoton cewa akalla mutane 40 ne iftila'in ya rutsa da su, an ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 15 ga watan Mayun 2024.

Shafi'u Abubakar, mai shekaru 38 da haihuwa ne mutumin da rundunar 'yan sandan Kano ta kama bisa zargin kunna wuta a masallacin Gezawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel