Sojan da Aka Fafata a Juyin Mulkin 1966 a Najeriya da Shi Ya Rasu a Yau

Sojan da Aka Fafata a Juyin Mulkin 1966 a Najeriya da Shi Ya Rasu a Yau

  • Tsohon Janar na sojoji wanda ya fafata a juyin mulkin shekarar 1966, Garba Duba ya kwanta dama a yau Juma'a
  • Duba wanda dan asalin jihar Niger ne ya mulki jihohin Bauchi da Sokoto a matsayin gwamna a lokacin mulkin soja
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Sanata Shehu Sani ya fitar a yau Juma'a a shafinsa na Facebook

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Tsohon Janar din sojoji a Najeriya, Garba Duba ya riga mu gidan gaskiya.

Duba wanda ya mulki jihohin Bauchi da Sokoto ya rasu ne a yau Juma'a 17 ga watan Mayu.

Tsohon Janar din soja ya rasu a Najeriya
Tsohon Janar a Najeriya, Garba Duba ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Bologi Ibrahim.
Asali: Facebook

Yaushe marigayi tsohon sojan ya rasu?

Kara karanta wannan

"Ko a jikina," Ministan Tinubu ya maida martani kan abubuwan da ke faruwa a Rivers

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani shi ya bayyana haka a yau Juma'a 17 ga watan Mayu a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin wanda ɗan asalin jihar Niger ne ya rasu yana da shekaru 82 a duniya bayan fama da jinya.

Shehu Sani ya ce tuni aka binne shi bayan sallar jana'iza a makabartar Gudu dake birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Jihohin da tsohon sojan ya mulka

Duba ya mulki jihar Bauchi a lokacin mulkin Cif Olusegun Obasanjo daga shekarar 1978 zuwa 1979.

A mukin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga 1984 zuwa 1985, Duba ya mulki jihar Sokoto.

Duba wanda yake matashi a lokacin juyin mulkin 1966, ya fafata a artabun da ya yi ajalin Johnson Aguiyi-Ironsi.

Marigayin ya yi ritaya a shekarar 1993 inda ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 98

Ya rike shugaban kamfanin New Nigerian Development (NNDC) da kuma kamfanin SGI da Leadway Pension Fund.

Hadimin gwamnan Niger ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya tura sakon jaje bayan rasuwar hadiminsa, Kwamred Muhammad Adam Erena.

Gwamnan ya bayyana mutuwar Erena wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar ne a matsayin babban rashi ga jihar.

Marigayin ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar ne a mulkin marigayi tsohon gwamna, Abdulkadir Kure wanda ya muki jihar daga 1999 zuwa 2007.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel