Abun Al Ajabi
Bishop David Oyedapo, Shugaban cocin Living Faith ya bayyana cewa tsawon shekaru 23 ba a taba dauke wutar lantarki ba a hedkwatar cocinsa da ke Ota, jihar Ogun.
Mista Kahinda Otafire, ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda, ya fada wani halin bayan ya furta wasu kalamai da ke nuna cewa talaka ba zai shiga aljanna.
An fara wannan tafiyar kan titi mai cin rai ne a 19 ga watan Afirilu sannan aka kammala a ranar 29 ga watan Mayu wanda wani mai babur Kunle Adeyanju ya fara.
Mutumin ya bayyana kansa a matsayin namijin duniya a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, yana mai cewa ba za a taba mantawa da tarihin da ya kafa ba.
Toko, wani masoyin kare kare ne dan kasar Japan, wanda ya nemi wani kamfani wanda ya kera masa suturar da ta canza masa kama ya koma tamkar kare saboda burinsa.
Wata matashiyar mata ta ceto ran wani matashi da ya so hallaka kansa bayan ta bashi makudan kudade kimanin N415k domin ya siya motar da ya ke burin mallaka.
An bar masu yawon bude idon baki bude cike da mamakin yadda wani mutum ya rasa yatsansa bayan zakin da ke cikin keji ya yi caraf da yatsan shi yana wasa da shi.
Wani mutumi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a makabarta. A cikin bidiyon da ke yawo, an gano shi tare da mutanen da ya gayyata a tsakanin kaburbura.
Wani yaro dan Najeriya ya samu doguwar rigar makaranta da ta girme shi daga telansa, lamarin da ya girgiza da yawan jama'a a kafafen sada zumunta na Twitter.
Abun Al Ajabi
Samu kari