Bidiyon yadda zaki ya cizge wa mai kula da shi yatsa, yana tsaka da kokarin birge 'yan mata
- Wani ma'aikacin gidan Zoo ya rasa yatsan shi na dama a kokarin da yayi na taba zaki da ke cikin keji domin birge mutane
- Mutumin wanda ke kokarin birge masu yawon bude ido an gan shi a bidiyo yana kokarin kwace yatsan shi daga bakin fusataccen zakin
- Bayan zakin ya saki hannunsa, an ga mai kula da gidan dabbobin ya tashi cike da tsananin radadi ya bar wurin domin ganin likita
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
An bar masu yawon bude idon baki bude cike da mamakin yadda wani mutum ya rasa yatsan shi bayan zakin da ke cikin keji ya yi caraf da yatsan shi yayin da yake wasa da shi.
Mai kula da namun dajin a wani gidan namun dajin da ke St. Jamaica Zoo ya hanzarta neman masana kiwon lafiya bayan masu yawon bude ido sun nadi lamarin a wayoyinsu.

Asali: UGC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalla mutane goma sha biyar ne suka shaida yadda lamarin ya faru kuma suka wallafa a shafukan sada zumunta.
Lamarin wanda aka nada a wayoyi tuni ya karade shafukan sada zumuntar zamani.
Kamar yadda masu lura na yanar gizo suka sanar, lamarin ya auku ne mintoci kadan kafin karfe hudu kuma da yawan masu ziyara sun gani.
Wani mai yawon bude ido ya ce mai kula da namun dajin ya yi yunkurin burge masu ziyara amma ya fusata zakin.
"A lokacin da lamarin ya faru, zato na wasa ne. Ban yi zaton da gaske bane. Ban zata da gaske ake komai ba saboda aikin shi ne. A lokacin da ya fadi kasa ne kowa ya gane da gaske yake. Kowa sai ya tsorata," yace.
Ihu daga mai kula da dabbobin
Ihun da mai kula da dabbobin yayi yayin da yake kokarin kwace yatsan shi daga bakin zakin ya gigita jama'a.
Wata ganau ta ce, "Dukkan fatar hannun sai da ta cire. Tserewa nayi daga wurin saboda bana son ganin jini."
Observer Online ta ruwaito cewa, cike da kuna da radadi mai kula da namun dajin ya tashi bayan lamarin kuma ya nufi motarsa domin barin wurin.
"Amma kuma a fuskarsa, tamkar babu radadin yayin da ya tashi kuma yake barin wurin," tace.
Asali: Legit.ng