Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba

Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba

  • An zargi Mwende Frey da mallakar gidan karuwai a fakaice a matsayin shagon aski bayan bidiyon da mata ke wa maza rawa yayin da ake musu aski ya bayyana
  • Sai dai, a cewarta sana'arta halastacciya ce kuma tana kokarin ganin ta bunkasa tare da bude wani shagon a cikin gari don biya wa mutanen da ba za su iya zuwa shagonta bukatarsu ba
  • Ta bayyana cewa, ba askin gashin kai kadai suka tsaya ba, suna iya askewa namiji kirji da sauran wuraren jikinsa da gashi ke fitowa yayin da ake masa tausa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata mata mai aski mai suna Mwende Frey ta bayyana yadda kasuwancinta yake tare da kalubalen da take fuskanta yayin da take gudanar da shagon mata zalla wadanda maza zalla suke wa aiki.

Kara karanta wannan

'Dan Allah ta ya zan samu Saurayi?' Wata kyakkyawar budurwa ta koka da zaman kaɗaici

A wata tattaunawa da Radio Maisha, mahaifiyar yaro dayan ta bayyana yadda tafi jin dadin harka da dattawa a shagonta saboda sun fi sakin kudi.

Mwende Frey, matar da ke da ashgon askin maza wanda mata ke musu rawa da tausa
Budurwa Mai Shagon Askin Da Mata Ke Wa Maza Rawa da Tausa, Tace Ba Kai Kadai Suke Askewa Ba. Hoto daga @mwendefrey
Asali: Twitter

Haka zalika, zankadediyar mai askin ta kara da cewa, shagon askinta na maza zalla ne sannan ta haramtawa matan da suke rako su shiga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan kai namiji ne, ka bar matarka, 'yar uwarka, ko abokiyar wasarka ko ma budurwarka a wajen adana motoci.
"Ba ma son matsala kuma yawancin mata nada matsala idan suka ga ana taba mazansu yayin musu aski a shagon," a cewarta.

Da aka tambayeta takamaiman abun da suke yi wa maza wanda ya halasta wandanda dokokin, a cewarta:

"Muna aske musu komai daga kai, kirji da abun da yayi kasa. Muna da masu yin tausa sannan bayan an gama wa namiji aski akwai mace da ke masa rawa tare da nishadantar da shi."

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Mwende ta bada labarin yadda wata mata tazo shagon askinta tare bude mata wuta saboda tana son sanin abun da mijinta ke yi a wajen.

"Ta tambaye mu idan mun taba ganin wani kamar haka, inda muka ce mata a'a, bamu taba ganin wani mai kama da shi ba, amma mun yi mata karya. Mijinta na ciki, bamu fada mata gaskiya ba saboda mutumin ya riga ya biya kudin,"

Ta kara da bayyana yadda take shirye-shiryen bude irin shagon a cikin gari domin wadanda ba za su samu damar zuwa Eastern bypass ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel