Bidiyon Kasaitacciyar Tawagar Tsadaddun Motocin Ciyaman a Kano Ya Janyo Cece-kuce

Bidiyon Kasaitacciyar Tawagar Tsadaddun Motocin Ciyaman a Kano Ya Janyo Cece-kuce

  • Injiniya Abdullahi Garba Ramat, shugaban karamar hukumar Ungogo ya tada kura a yanar gizo bayan bidiyon jerin tsadaddun motocin da suke masa rakiya ya yadu
  • Bidiyon da aka gani a shafinsa na Facebook, an ga jerin wasu rantsatstsun motoci, wadanda mallakin injiniyan ne suna tafe a jere cike da kasaita
  • An yi ta cece-kuce karkashin bidiyon, yayin da wasu masu amfani da kafafen sada zumuntar zamani suke ganin hakan bai kyautu ba wanda ya jawo masa caccaka daga garesu

Kano - Wani bidiyo da ya bayyana na nuna jerin rantsatsun motocin wani shugaban karamar hukuma a jihar Kano, wanda ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Injiniya Abdullahi Garba Ramat, wanda shi ne shugaban karamar hukumar Ungogo wanda ya dira daga jerin rantsatstsun motocinsa, kamar yadda bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

'Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon jerin kasaitattun motocin, inda wasu masu amfani da yanar gizo suka siffanta hakan da barnata dukiyar al'umma, yayin da wasu suka koka a kan cewa jerin motocin ba su cancanci shugaban karamar hukuma ba.

Legit.ng ta kasa gano wanne taro ya dosa ko a inda aka dauki bidiyon har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama'ar sun yi martani

@collins.blac ya ce: "Shugaban karamar hukuma kawai. Idan fa ya samu damar zama gwamnan jihar Kano."
@gerald_boychi ya ce: "Wadannan su ne 'yan arewan ku, suna barin wasu cikin matsanancin talauci, wasu kuma cikin arziki."
@sheddi_bankz ya ce: "Yanzu kalli yanayin garin, da haka ne kasan irin talaucin da mutum yake fama da shi, ba wai da hawa motoci da yawa ba."
@dipzongs ya ce: "A kasa mai hankali, wadannan 'yan siyasan ne za su yi irin wannan wallafar, amma ba zai iya cin jarabawar gwajin tuki ba balle a yi maganar zama shugaban karamar hukuma ko yanki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel