Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista

  • Ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda, Mista Kahinda Otafire, ya bayyana cewa talakawa ba za su shiga aljanna ba
  • Ya sanar da cewa, yawan korafin da talaka ke kaiwa Ubangiji da koke a kowacce rana ne yasa ba za a shigar da shi aljanna ba
  • Ya yi kira ga dalibai da su mike su nemi kudi tun da karfinsu a maimakon su yi ta kai koke da korafe-korafe

Mista Kahinda Otafire, ministan harkokin cikin gida na kasar Uganda, ya fada wani hali bayan ya furta wasu kalamai da ke nuna cewa talaka ba zai shiga aljanna ba.

Ministan ya ce, talaka ba zai shiga aljanna ba saboda suka da yake yi Ubangiji wurin mika kokensa a kowacce rana, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista
Talaka ba zai shiga aljanna ba saboda yawan korafinsa, Minista. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan a lokacin jawabin da ya yi yayin wani taron dalibai a Kyenjojo, ya sanar musu da cewa kada su zargi Ubangiji idan sun gaza amfani da damar da ya basu na yakar takaici inda ya shawarce su da su dage wurin neman arziki a madadin korafin da suke yi a kowacce rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Otafire ya ce kuskure ne jama'a su dinga korafi da zargin Ubangiji ba tare da sun tashi tsaye wurin yin ayyukan da za su samar musu da kudi ba.

Ministan ya kara da cewa, halayyar sukar Ubangiji da talakawa ke yi ita za ta hana su shiga aljanna.

Babu shakka wannan lamarin ya janyo cece-kuce inda wasu Malaman addinai da kungiyoyi suke zargin gwamnati da gazawa wurin samar da yanayi mai kyau da har talakawa za su samu sassauci daga halin matsin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

Uganda tana daya daga cikin kasashe masu yawan matasa da ba su da aikin yi.

Maciji ya sari magidanci yayin da yake zaune a masai yana latsa wayarsa

A wani labari na daban, wani maciji da ya dade yana kwantan bauna a bandakin wani mutum ya sare sa a mazaunensa yayin da mutumin ke kan tukunyar masai rike da wayarsa yana wasa da ita. Sabri Tazali, daga kasar Malaysia ya rayu bayan farmakin da macijin ya kai masa, Shafin LIB ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana bayan farmakin da macijin ya kai masa ya yi "sa'a" kasurgumin macijin bai sare sa a al'aurarsa ba.

Macijin ya sari Tazali, mai shekaru 28 yayin da yake tsaka da amfani da bandaki a gidansa cikin garin Selayang a jihar Selangor dake kasar Malaysia inda yaji wani irin sara mai kaifi a mazaunensa. Bayan yaji alamar sarar macijin a mazaunensa, Tazali ya yi hanzarin mikewa gami da cafko macijin tare da buga sa da bangon bandakin.

Kara karanta wannan

Gumi ga Deliget: Cin hancin da za ku karba ba zai kare ku daga rashin tsaron Najeriya ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel