Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta

Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta

  • Wata jarumar masana'antar shirya fina-finai na Nollywood, Mama Rainbow ta wallafa bidiyon wani abun al'ajabi da ya faru a cocinta kwanan nan a shafukan sada zumuntar zamani
  • Dattijuwar a cikin farar rigar wankanta ta rike jinjirar tare da bukatar mutane su bude idanuwansu su ga sunan Allah da aka rubutu a yaren larabci a kunnuwanta
  • Wallafar Iya Rainbow ta janyo cece-kuce a yanar gizo yayin da mutane da dama suka ki yarda da ita tare da tuhumar siddabarun da ke tare da bidiyon

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitacciyar jarumar wasan kwaikwayo, Mama Rainbow wacce kuma jagoran wata coci ce, ta wallafa wata mu'ujizar Ubangiji ta hanyar daya daga cikin jinjiran da aka haifa a cocinta.

A wani bidiyo da ya yi yawo a yanar gizo, an ga jarumar rike da wata jinjira, inda ta ke bayanin da Yarbanci yadda wani Musulmi ya nuna wani irin zane a kunnen jinjirar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta
Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta. Hoto daga @Instablog9ja
Asali: Instagram

Mama Rainbow ta bukaci mutane su bude idanuwansu su ga rubutun 'Allahu' a kunnuwan jinjirar da tayi bacci cikin kwanciyar hankali yayin da aka nunata a kafafan sada zumuntar zamani.

Jarumar ta yi godiya ga Ubangiji yayin da ta nuna mu'ujizar da Ubangiji ya albarkaci taron jama'arta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama'a sun yi martani

Martanin jama'a:

jouceisy: "Wadannan kawai surar gurin guntsinta ne ranki shi dade. Addini ba zai kashemu ba a kasar nan!"
united fc99: "Ni ba zan ce komai ba."
iam_horpeyhemi: "Kila wasan kwaikwayo ne ko wani abu daban."
mcelvisjcfrn: "Ku taru a nan idan kun lura da kyan jinjirar ba tare da damuwa da sanyin Zobon ba."
godson21100: "Abun dariya. Wannan shi ne makurar jahilci. Tare da bada girma yadda ya dace ranki shi dade."

aforchibunduaugustine: "Ni fa ban ga komai ba.. mummy wa... Idan zan ci ki gyara... haka kunnuwa suke!!! wai me addini zai mana ne!!!

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

Hotuna: 'Dan Najeriya ya Tsinta Abarba a Teku Dauke da Hoton Saurayi da Budurwa an Dinke

A wani labari na daban, wani mai amfani da shafin Twitter da @TheOnlyCleverly ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar bayan ya wallafa wani kulunboton sihiri da aka yi don hada wasu masoya inda ya gani a gefen wata teku.

Sihirin hada masoyan shi ne hotuna biyu na mace da namiji da aka daure cikin wata abarba, wanda mutane da dama sun yi imani an yi ne don a haddasa matsananciyar kauna mai dorewa tsakanin masoyan biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel