Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata

Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata

  • Wani matashi wanda ya so kashe kansa saboda rashin cimma burinsa a rayuwa ya samu mafarkinsa ya zama gaskiya
  • Mutumin ya ce burinsa shine ya mallaki mota kuma yana ta fama da matsalar damuwa sannan baya so ya farka a duniya
  • Sai dai, wata matashiya da ya hadu da ita ta kai masa dauki inda ta bashi fulawowin da ke nuna ana son shi da kuma kudi N415k

Wani matashi da ya gaji da duniya har yake ji kamar kada ya farka daga bacci saboda damuwa ya samu taimako.

Mutumin na da burin ganin ya mallaki mota nasa na kansa amma bai cimma wannan kudiri ba.

Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata
Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata Hoto: @worthfeed.
Asali: Instagram

Ya samu makudan kudade

A wata rana, yace yana ta tunanin kashe kansa saboda yana fama da matsala ta damuwa. Amma a kan hanyarsa sai ya hadu da wata matashiyar mata sannan ta taimaka wajen cika masa daya daga cikin burikansa na siyan mota wanda kudinsa ya kai naira dubu 415.

Kara karanta wannan

Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashiyar ta gabatar masa da fulawowi sannan ta mika masa makudan kudade don haka ya canja shawarar ci gaba da rayuwa.

A cikin wani bidiyo mai taba zuciya da aka saki, an gano inda ya fashe da kuka a lokaci da kudade da fulawowin suka shiga hannunsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya Instagram sun yi martani

@ cdero26 ya ce:

"Ku biya gaba. Ba ku da masaniyar halin da wasu mutane ke ciki. Allah ya saka da alheri."

@dewisanchez yayi sharhi:

"Kyautatawa ga wasu na iya ceto ran wani."

@michellefield4 ya yi martani:

“Ka sa wani farin ciki. Zai fi mana dukkanmu mu wanzar da soyayya da farin ciki ga duk mutumin da muka hadu da shi!! A ci gaba da haka. Dole ne mu taimaki junanmu, duk ana tare!!"

Kara karanta wannan

Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani

@paula_twin_2 ya ce:

"Hakan ya sa ni kuka. Akwai kyawawan mutane a duniyar nan suna yin abubuwan ban mamaki ga sauran mutane."

Adam Zango ya saki zafafan hotunansa tare da amaryarsa yayin da suka cika shekaru 3 da aure

A wani labarin, a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayu ne shahararren dan wasan nan na Hausa kuma mawakin zamani, Adam A. Zango ya cika shekaru da auren amaryarsa, Safiya Chalawa.

Adam Zango ya raya wannan rana ta musamman inda ya saki wasu zafafan hotunansa da matar tasa domin murnar wannan tafiya da ta fara mika a rayuwarsu.

Ana ganin wannan murna tasa ba zai rasa nasaba da yadda suka shafe tsawon shekaru uku ba tare da an ji kansu da amaryar tasa ba sakamakon lakabi da ake masa da mai yawan auri-saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel