Abun Al Ajabi
Kotun ta gano cewa babu wani uzuri da za a iya yi wa matar mai shekara 28, hakan na nufin ba za a sake ta ba idan ta kammala zaman shekara 15 da aka yanke mata.
Wani magidanci wanda ya ce ya gaji da rigimar matarsa ya roki yan sanda da su kama shi su tsare shi a kurkuku domin hakan zai fiye masa zama da matarsa a gida.
Rundunar yan sandan Benue ta sanar da mazauna jihar kan wani sabon salon ta’addanci da wasu da ba’a san ko su wanene ba ke amfani da shi wajen kashe yan mata.
Wani matashi mai suna Aliyu Idris, ya bayyana cewa a shirye yake ya siyar da kansa saboda halin da ya tsinci kansa a ciki na kunci, radadi da matsin rayuwa.
Idan da ranka za ka sha kallo. Wani bidiyo da muka samu ya nuna yadda wasu ma'aurata suka bayyana cewa, sun sayi gida daga wani gari kuma suka kawo shi garinsu.
Matar mai suna Jivunben Rabari wacce ke da shekaru 70 a duniya ta kasance daya daga cikin uwayen da suka samu haihuwarsu ta farko a shekarun tsufa a duniya.
An kera tukunyar ne gida biyu ta yadda mutum zai iya dafa abinci iri biyu a lokaci guda domin saukaka rayuwa musamman a yanzu da ake tsadar abubuwan girki.
Wani mutumi mai suna Haruna Buba mai shekaru 32, ya kashe mahaifinsa a ranar Asabar a kauyen Zange da ke karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe a kan wata gona.
Dubun wasu samari ta cika, jami'an yan sanda reshen jihar Ogun sun cafke samari uku kan zargin kashe wani ɗan Okada da kuma sace mashin ɗinsa a jihar ta Ogun.
Abun Al Ajabi
Samu kari