Bidiyon yadda wani matashi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwara a makabarta, mutane da dama sun halarci taron

Bidiyon yadda wani matashi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwara a makabarta, mutane da dama sun halarci taron

  • Wani matashi ya kara shekara daya a rayuwarsa don haka ya yanke shawarar raya wannan rana a makabarta
  • A wani bidiyo da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, an gano uban taron da abokansa suna shakatawa a tsakakkanin kaburbura
  • Dukkanin wadanda suka halarci sun kasance sanye da fararen tufafi yayin da suka dunga daukar hotuna don tarihi

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na wani bikin zagayowar ranar haihuwa da aka gudanar da makabarta.

A bidiyon wanda shafin @cocoacitytv ya wallafa a dandalin TikTok ya nuno mahalarta taron suna shakatawa a tsakakkanin kaburbura.

Bidiyon yadda wani matashi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwara a makabarta, mutane da dama sun halarci taron
Bidiyon yadda wani matashi ya yi bikin zagayowar ranar haihuwara a makabarta, mutane da dama sun halarci taron Hoto: TikTok/@cocoacitytv
Asali: UGC

Hakazalika dukkanin wadanda suka halarci taron sun kasance sanye da fararen tufafi wanda ga dukkan alamu shine ankon bikin.

Kara karanta wannan

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

An kuma jiyo sautin kida yana tashi a cikin bidiyon yayin da mahalarta taron ke daukar hotuna tare da uban taron da kek dinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An daura kek din a kan wani teburi bayan an lullube shi da farin kyalle da lemuka iri-iri jere a kansa.

Jama’a da dama sun cika da al’ajabin dalilin da zai sa uban gayyar ya zabi makabarta domin raya wannan rana.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

June Konadu Thursda ya ce:

“Sun yi sa’a makabartan na a cikin gari ne don haka suka wataya, inama ace wannan taron a makabartar wasu kauyuka aka yi.. da an ga gudun fanfalaki."

priscillaaryee702gmail.0 ya ce:

“Idan ka tuna ranar haihuwarka toh dole ka tuna ranar mutuwarka, hakan ya yi kyau dan uwa da ku tuna cewa suma kamar mu ne.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

AMADI ASARE ya ce:

“Ina ganin ya kamata mu dunga tambayoyi kamar, shin yana da kyau cin abinci a makabarta ko babu kyau? Muna iya tambayan kakanni da iyayenmu.”

Dankwali ya ja hula: Bidiyon wata amarya yayin da take yiwa angonta budar kai ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, kamar yadda yake bisa al’adar mallam Bahaushe, a kan yi budar kai a yayin shagalin bikin aure, inda ango zai bude fuskar amaryarsa bayan ya baiwa kawayen amarya tukwici.

Sai dai lamarin ya sauya salo a wani bikin aure da aka yi kwanan nan, inda dankwali ya ja hula.

A wani bidiyo da ya yi fice a shafukan soshiyal midiya, an gano yadda aka yi budar kan ango sabanin na amarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel