Abuja
Bola Tinubu ya yi fatali da maganar dawo da tallafin mai duk da korafi da ake ta yi kan haka a ƙasar inda ya ce matakin ya jefa al'umma a kunci amma ya zama dole.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da gwamnatinsa su zo a hau kan teburin sulhu domin a samo mafita.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya a ranar Lahadi. Shugaban kasan zai yi jawabin ne yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin kasa.
Jami'an tsaro sun tarwatsa matasan da ke gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja. Jami'an tsaron sun kuma cafke 'yan jaridan da ke wajen.
Jami'an tsaro sun yi ta harbe-harbe kan masu zanga-zanga domin tarwatsa su a birnin Abuja inda suka kutsa cikin filin wasa na MKO Abiola a yau Asabar.
Gwiwar jama'a ta fara sanyi yayin da aka samu karancin masu ci gaba da zanga-zanga a rana ta uku a baban birnin tarayya Abuja yayin ko mutum daya bai fito ba.
Rahotanni sun nuna ƴan sanda sun buɗe wuta a saman iska a lokacin da uka fatattaki tsirarun masu zanga zanga a filin wasa na Moshood Abiola a Abuja.
Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar Abuja ta yi martani kan zargin daukar nauyin masu zanga-zanga inda ta ce tsohon faifan bidiyo ake yadawa kan lamarin.
Gwamnatin tarayya ta musanta cewa ta na da hannu cikin matsalolin sadarwa da ake fuskanta a kasar nan, duk da kalubale da aka fuskanta dab da zanga-zanga
Abuja
Samu kari