'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Birnin Tarayya Abuja, Sun Gamu da Matsala

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Birnin Tarayya Abuja, Sun Gamu da Matsala

  • Ƴan bindiga sun sake kai hari yankin birnin tarayya Abuja, sun yi yunƙurin garkuwa da mutane 20 a daren jiya Lahadi
  • Kwamishinan ƴan sandan FCT da kansa ya jagoranci dakarun ƴan sanda suka kai ɗauki kuma suka yi nasarar dakile harin
  • Sai dai har yanzu ba a gano wasu daga cikin mutanen da maharan suka ɗauko ba, ƴan sanda sun bazama domin a ceto su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutanen kauyen Dawaki da ke kusa da Kubwa a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar wata majiya, an yi garkuwa da mutane 20 a ƙauyen, lamarin da ya haifar da tashin hankali da fargaba a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga yanayi yayin da ƴan bindiga suka kashe sojojin Najeriya

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan sanda sun dakile harin garkuwa da mutane a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun dura birnin Abuja

Daily Trust ta ruwaito cewa miyagun ƴan bindigar sun farmaki gidajen mutane a layin Frank Opara gabanin jami'an tsaro suka kawo ɗauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban yankin Dawaki Rock Heaven, Tunde Abdulrahim, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na daren ranar Lahadi.

Abdulrahim ya ce ‘yan bindiga kusan 50 dauke da makamai da suka ƙunshi maza da mata, sun farmaki ƙauyen inda suka shiga kusan gidaje shida.

Ƴan sanda sun daƙile harin Abuja

Da take tsokaci game da harin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Benneth Igweh, ya jagoranci ‘yan sanda zuwa wurin.

Ta bayyana cewa CP Igweh da kansa ya jagoranci ƴan sanda suka yi artabu da masu garkuwa da mutanen kuma suka samu nasara.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: An samu ƙarin mutanen da suka mutu a harin da aka kai Masallaci a Kano

"Nan take bayan samun labarin ƴan bindiga sun shiga Dawaki, kwamishinan ƴan sanda CP Igwe da kansa ya jagoranci ƴan sanda suka kai ɗauki.
"Dakarun ƴan sandan da haɗin guiwar mafarauta sun tari maharan a Ushafa Hill, inda suka yi musayar wuta wanda ya sa suka arce ɗauke da raunuka kuma aka ceto mutanen da suka sace.
"Duk da har yanzun mutum ɗaya na kwance a asibiti, kwamishinan ƴan sanda ya jaddada shirin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Abuja."

- SP Josephine Adeh

Adeh ta ƙara da cewa yanzu haka ƴan sanda na ci gaba da ƙoƙarin ceto mutanen da ƴan bindigar suka sace, waɗanda suka tsere yayin musayar wuta, Premium Times ta ruwaito.

An kashe sojoji 2 a Abia

A wani rahoton kuma, Gwamna Alex Otti ya yi jimamin mummunan harin da aka kashe sojoji biyu a Aba ta jihar Abia tare da alƙawarin kamo masu hannu a laifin.

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe mutune uku a harin gabanin dakarun sojoji su yi nasarar fatattakar su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel