Bayan Soke Harajin Yanar Gizo, Gwamnan CBN Ya Biyo Wata Hanya, Ya Kara Kudin Ruwa

Bayan Soke Harajin Yanar Gizo, Gwamnan CBN Ya Biyo Wata Hanya, Ya Kara Kudin Ruwa

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Babban Bankin Najeriya, CBN ya sake kara kudin ruwa a kasar nan
  • Bankin ya kara kuɗin ruwa daga 24.75% zuwa 26.25% wanda ya kasance kari na uku kenan a cikin wannan shekara
  • Hakan na zuwa ne bayan soke biyan harajin yanar gizo da bankin ya yi bayan korafe-korafe da ake ta yi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ta kara kudin ruwa daga 24.75% zuwa 26.25% a kasar.

Gwamnan babban bankin a Najeriya, Yemi Cardoso shi ya bayyana haka a yau Talata 21 ga watan Mayu.

CBN ya sake kara kudin ruwa a Najeriya
Babban Bankin Najeriya, CBN ya kara kuɗin ruwa zuwa 26.25%. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Asali: Facebook

Tsarin da CBN yake bi a karin

Kara karanta wannan

Emefiele: “Yadda na biya cin hancin $600, 000 domin a biya ni kudin kwangila a CBN”

Bankin ya yi amfani da Monetary Policy Rate (MPR) wanda shi ne mizanin ƙiyasta kudin ruwa da CBN ke amfani da shi, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN ya yi amfani da Monetary Policy Rate (MPR) wanda shi ne mizanin ƙiyasta kudin ruwa da CBN ke amfani da shi.

Hakan ya biyo bayan hauhawan farashin kaya ya tashi a Najeriya da 33.69% a ranar 15 ga watan Mayu, cewar TheCable.

Karin harajin da CBN ya yi a shekara

Har ila yau, wannan shi ne karo na uku a cikin wannan shekara da bankin ke kara kuɗin.

Wannan na zuwa ne bayan bankin ya soke biyan harajin yanar gizo da ya kakabawa ƴan kasar a kwanakin baya.

Karin biyan harajin ya rikita ƴan kasar inda suka yi ta korafi kan halin da suke ciki tun kafin karin harajin.

Kara karanta wannan

Wike v Fubara, Ganduje v Abba da wasu manyan gwabzawar da ake jira a 2027

Daga bisani bankin ya yi karin haske kan hada-hadar kudi 16 da harajin zai shafa domin wayar da kan jama'a.

Tinubu ya dakatar tsarin haraji na CBN

A wani labarin, an ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da biyan harajin tsaron yanar gizo a Najeriya.

Tinubu ya dauki matakin ne bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo tsarin biyan harajin 0.5% kan masu tura kudi bankuna.

Shugaban ya ce ya damu da halin da 'yan ƙasar ke ciki kuma ba zai bari a kara musu wata wahala ba a halin da suke ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel