Jam’iyyar PDP Ta Bayyana Wanda Zai Jagoranci Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Edo

Jam’iyyar PDP Ta Bayyana Wanda Zai Jagoranci Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Edo

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai jagoranci kwamitin PDP mai mutane 152 a yakin neman zaben gwamnan Edo
  • Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Abuja
  • Kwamitin ya kunshi tsofaffin mataimakan shugaban kasa da gwamnonin PDP, za a gudanar da zaben Edo ne a Satumbar 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar PDP ta kafa kwamiti mai mambobi 152 domin yakin neman zaben gwamnan Edo da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Satumba.

PDP ta yi magana kan kwamitin yakin zaben Edo
Gwamna Fintiri zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben PDP a zaben gwamnan Edo. Hoto: @GovernorAUF
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya kafa tarihi, ma'aikata za su sha romon mafi ƙarancin albashi bayan shekaru

Fintiri zai jagoranci kwamitin PDP

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin na karkashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ologunagba ya ce za a kaddamar da kwamitin ne a ranar 11 ga watan Yuni, 2024.

Kakakin jam'iyyar ya ce kwamitin gudanarwa na kasa na PDP ya dukufa wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben Edo.

Mambobin kwamitin yakin zaben PDP

Sauran 'yan kwamitin yakin neman zaben sun hada da Gwamna Kefas Agbu na Taraba da Sheriff Oborevwori na Delta a matsayin mataimakan shugabanni, da kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Sauran sun hada da tsofaffin mataimakan shugaban kasa Atiku Abubakar da Namadi Sambo, da wasu tsofaffin gwamnoni na jam’iyyar PDP, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Haka zalika, akwai shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, Sen. Adolphus Wabara, da mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagun, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Jarirai 21,000 na mutuwa a kowane wata a Najeriya, gwamnan Kaduna ya fadi dalili

PDP ta tsayar da dan takarar Edo

Tun da fari, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta zabi Asue Ighodalo a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Edo a zaben jihar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Satumba.

Asue Ighodalo ya samu nasarar doke ƴan takara tara ciki har da mataimakin gwamna na lokacin watau Philip Shaibu.

Jam'iyyar PDP ta gudanar da zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Edo ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel