Tinubu Ya Janye Naɗin Yaron Ministansa Bayan Surutu Kan Muƙamin, Ya Maye Gurbinsa

Tinubu Ya Janye Naɗin Yaron Ministansa Bayan Surutu Kan Muƙamin, Ya Maye Gurbinsa

  • Yayin da aka yi ta ce-ce-ku-ce kan nadin na hannun daman Nyesom Wike, Shugaba Bola Tinubu ya janye nadin da ya yi
  • Tinubu ya maye gurbin Chukwuemeka Woke da Dakta Adedeji Ashiru a matsayin daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin
  • Yayin da shugaban kasar ya ji korafe-korafen jama'a, ya mayar da Woke zuwa hukumar da ke kula da mai ta NOSDRA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sauya sunan na hannun daman Nyesom Wike da ya nada mukami kwanan nan.

Tinubu ya cire sunan Chukwuemeka Woke a matsayin babban daraktan hukumar Ogun-Osun River Basin bayan cece-kuce da aka yi.

Kara karanta wannan

"Da wahala", Jigon APC ya gaji da kame kamen Tinubu wajen gyara Najeriya kamar Lagos

Tinubu ya janye nadin yaron Wike muƙami bayan cece-kuce da aka yi
Bola Tinubu ya maye gurbin yaron Nyesom Wike bayan cece-kuce da ake yi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Nadin da Tinubu ya yi ya jawo matsala

Shugaban ya nada Woke ne wanda tsohon shugaban ma'aikatan Nyesom Wike ne lokacin da ya ke gwamnan a jihar Rivers a ranar 9 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai nadin ya ci karo da cikas bayan korafe-korafen da ake ta yi da cewa mukamin ya saba tsarin yankin.

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da sauya Woke a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Ajuri ya ce an maye gurbin Woke da Dakta Adedeji Ashiru yayin da aka mayar da shi hukumar kula da mai ta NOSDRA.

Tinubu ya maye gurbin yaron Wike

"Woke bayan kasancewarsa injiniya, masani ne kan muhalli kuma gogaggen dan siyasa."
"Ya rike mukamin shugaban ƙaramar hukumar Emohua da kuma shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Rivers na tsawon lokaci."

Kara karanta wannan

Fitaccen Basarake a Najeriya ya cire tsoro, ya zargi EFCC da karbar rashawa

"Dakta Ashiru ya yi karatu a Jami'ar Common Wealth da ke Burtaniya wanda ya yi aiki da kamfanoni da dama."
"Tinubu ya bukaci wadanda aka naɗa mukaman da su yi amfani da kwarewarsu wurin inganta hukumomin da kuma aiki cikin gaskiya."

- Ajuri Ngelale

Tinubu ya naɗa na hannun daman Wike

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban ma'aikatan Nyesom Wike mukami a Najeriya.

Tinubu ya naɗa Chukwuemeka Woke a matsayin shugaban hukumar Ogun-Osun River Basin a ranar 9 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel