'A Biya Mu Hakkokinmu,' Yan Sanda da su Kayi Ritaya Sun yi Zanga Zanga

'A Biya Mu Hakkokinmu,' Yan Sanda da su Kayi Ritaya Sun yi Zanga Zanga

  • Wasu daga cikin jami’an ‘yan sandan da su ka yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja domin tunatar da gwamnati halin da su ke ciki
  • Tsofaffin ‘yan sandan Najeriyan sun bayyana cewa yanzu haka an shafe wata da watanni ba a biya su ko sisin kwabo daga hakkinsu ba duk da halin matsin da ake ciki
  • A zanga-zangar da aka gudanar a gaban majalisar dokokin kasar nan sun yi rokon gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sauya tsarin da ake biyansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Wasu daga tsofaffin jami’an ‘yan sandan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja domin bayyana korafinsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kaddamar da mummunar hari a Plateau, an kashe mutane 40

‘Yan sandan da su kayi ritaya karkashin shirin karo-karo na contributory pension scheme sun gudanar da zanga-zangar ne a harabar majalisar dokokin kasar nan.

IGP Kayode
'Yan sandan da su ka yi ritaya sun yi zanga-zanga a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Channels Televsion ta wallafa cewa ‘yan sandan da su ka kammala aikin tsaron rayukan ‘yan Najeriya sun shafe watanni ba a biya su ko sisi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'A biya mu fanshonmu' - Tsofaffin 'Yan sanda

Wasu daga ‘yan sandan kasar nan da su ka yi ritaya sun taru a gaban majalisar dokoki da ke babban birnin tarayya Abuja suna tunawa gwamnati hakkinsu na fansho.

Freedom radio ta ruwaito cewa ‘yan sandan masu ritaya sun taru rike da kwalaye domin nuna halin da su ke ciki.

'Yan sanda na wahala bayan ritaya

Tsofaffin jami’an sun tunatar da gwamnati irin mawuyacin halin da ake ciki, da bukatar a waiwayesu domin su samu waraka.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in kwastam a Abuja

Sun nemi gwamnati ta gaggauta sauya tsarin da ake biyansu, tare da rokon sufeton janar din 'yan da kada a hada hannu da shi wajen murkushe su.

Tsofaffin ‘yan sanda daga jihohi 27 ciki har da babban birnin tarayya Abuja ne su ka fito zanga-zangar.

Kano: ‘Babu batun rashin tsaro,’ Gwamnati

A baya mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin cewa akwai rashin tsaro a jihar, inda ta ce babu kamshin gaskiya cikin labarin.

Mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ne ya musanta haka, tare da bayar da tabbacin Kano na daga jihohi mafi kwanciyar hankiyar a Afrika ta yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.