Bola Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami Kabir Mohammed da Tayyib Odunowo a matsayin shugabannin FAAN da NAMA tare da maye gurbinsu da wasu nan take.
Gwamnatin Tarayya ta caccaki Bankin Duniya kan kalamansa game da biyan kudaden tallafin mai inda ta ce babu maganar ci gaba da biyan tallafin mai har abada.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami dukkan daraktocin ma'aikatar harkokin jiragen sama kwana daya bayan korar shugaban hukumomin FAAN da NAMA a jiya Laraba.
Dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Usman Ibrahim ya yi fatali da jami'yyar PDP inda ya koma jam'iyya mai mulki ta APC a jihar, ya yabawa salon mulkin Uba Sani.
A'ummar garin Tudun Biri, da sojoji suka yi sakarwa bama-bamai da ya kashe akalla mutum 100 sun musanya shigar da gwamnatin Tinubu kara kotu da neman diyyar N33bn.
Ma'aikatar bunkasa ma'adanan Najeriya ta roki majalisar tarayya da ta kara mata Naira biliyan 250 a kasafin kudin 2024 da za a ba ta. A yanzu an ba ma'aikatar N24bn.
Tun ba yau ba, ana yawan zargin NNPCL da cewa su na boye gaskiyar cinikinsu. Ba a san gaskiyar abin da ke faruwa game da kudin da ake samu wajen saida man fetur ba.
Sabanin yadda ake ta yada jita-jita a shafukan sada zumunta, jam’iyyar LP ba ta nemi babban jigon ta, Peter Obi ya nemi afuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Bankin duniya ya ce bude kofa domin shigo da kaya kamar shinkafa zai taimaka. Hakan zai sa a fito da mutane miliyan 1.3 daga cikin talauci da ake fama da shi.
Bola Tinubu
Samu kari