Tsohon Shugaban Kamfanin NNPCL Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 84, Bayanai Sun Fito

Tsohon Shugaban Kamfanin NNPCL Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 84, Bayanai Sun Fito

  • Kamfanin man NNPCL ya sanar da mutuwar tsohon shugabansa, Dakta John Maurice Thomas a yau Alhamis
  • NNPCL ya fitar da sanarwar ce a shafin X inda ya bayyana Thomas a matsayin wanda ya kware a fannin iskar gas
  • Marigayin shi ne ya rike shugabancin kamfanin na biyar wanda ya gaji kujerar marigayi Dakta Aret Adams

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPCL ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 84.

Marigayin Dakta Thomas John Maurice ya rasu ne a yau Alhamsi 14 ga watan Disamba bayan fama da doguwar jinya.

Tsohon shugaban kamfanin NNPCL ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 84 a duniya. Hoto: NNPCL.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rike mukami a NNPCL?

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya nada tsohon soja a matsayin shugaban hukumar Hisbah, ya fadi dalili

Thomas shi ne ya rike shugabancin kamfanin na biyar wanda ya gaji kujerar marigayi Dakta Aret Adams.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da NNPCL ya fitar a shafin X a yau Alhamis 14 ga watan Disamba.

Marigayin ya mulki kamfanin har na tsawon shekaru biyu daga watan Afrilun shekarar 1990 zuwa watan Yunin 1992, cewar Daily Post.

Wace sanarwa kamfanin NNPCL ya fitar?

Har ila yau, marigayin ya rike mukamai da dama da su ka hada da hukumar SAPETRO da kuma babban darakta a bankin UBA.

Sanarwar ta ce:

"A madadin kamfanin man NNPCL da ma'aikatansa da shugabansa, Mista Mele Kyari su na tura sakon jaje ga iyalai da 'yan uwan mamacin.
"Mu na addu'ar ubangijgi ya masa rahama, ya sa ya huta."

Sanarwar ta kuma bayyana Thomas a matsayin hazikin ma'aikaci wanda ya ba da gudunmawa musamman ta bangaren iskar gas inda shi ne layin da ya fi kwarewa.

Kara karanta wannan

Kano: EFCC ta gurfanar da ma'aurata kan handame miliyan 410, ta bayyana yadda abin ya faru

Shugaban karamar hukumar Gombe ya rasu

A wani labarin, shugaban karamar hukumar Gombe, Alhaji Usman Haruna ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin wanda aka fi sani da "Ali Ashaka' ya rasu ne a ranar Talata 5 ga watan Disamba a kasar Masar bayan fama da jinya.

Wannan na zuwa makwanni kadan bayan rasuwar babban limamin masallacin Izala da ke Unguwar Abuja, Imam Abubakar Sa'id a cikin birnin Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel