Kasafin 2024: Minista Na Rokon Majalisa Ta Karawa Ma’aikatarsa Naira Biliyan 250

Kasafin 2024: Minista Na Rokon Majalisa Ta Karawa Ma’aikatarsa Naira Biliyan 250

  • Ma'aikatar bunkasa ma'adanan Najeriya ta roki majalisar tarayya da ta kara mata Naira biliyan 250 a kasafin kudin 2024 da za a ba ta
  • Monistan ma'aikatar, Dele Alake ya yi rokon yayin kare kasafin Naira biliyan 24 da aka ware wa ma'aikatar, kudin da ya ce ba za su ishe su ba
  • A cewar Mr Adeleke, dole ne a ware wa ma'aikatar kaso mai tsoka daga kasafin kudin ma damar gwamnati na son cimma muradin farfado da tattalin arziki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan bunkasa ma'adanan kasa, Dele Alake, ya ce ma'aikatarsa na bukatar Naira biliyan 250 don hako ma'adanai amma gwamnati ta ware masa Naira biliyan 24.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 sun koka da kasafin kudin 2024, abin da Tinubu ya ware masu ya yi kadan

Mr Alake ya bayyana hakan a taron kare kasafin kudin 2024 da ke gudana a zauren majalisar tarayya karkashin kwamitin ma'adanan kasa a ranar Laraba.

Ministan Tinubu na neman karin Naira biliyan 250
Akan bukatar karin Naira biliyan 250, Mr Alake ya ce dole gwamnati ta zama kan gaba wajen hakar ma'adanai. Hoto: Dele Alake
Asali: Twitter

Akan bukatar karin Naira biliyan 250, Mr Alake ya ce dole gwamnati ta zama kan gaba wajen hakar ma'adanai, maimakon kyale kamfanoni suna cin karensu ba babaka a harkar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa ministan Tinubu ke neman karin kudi a kasafin 2024?

Ya bukaci 'yan majalisun da su amince da karin kudaden, inda ya tabbatar masu da cewa zai yi aiki tukuru don kwalliya ta biya kudin sabulu, Premium Times ta ruwaito.

Ya ce:

"Kudin da aka ware mana yanzu ba zai isa mu aiwatar da ko da abu daya daga kudurorinmu ba. Muna bukatar hako ma'adanai sosai, ba za mu sakarwa kamfanoni ragamar komai ba.
"Idan har da gaske muke kan farfado da tattalin arziki, to dole a ware wa ma'aikar ma'adanai Naira biliyan 250."

Kara karanta wannan

Abba: Kasafin kudin Sarakuna 4 ya haddasa hayaniya tsakanin ‘yan Majalisar jihar Kano

Ministan ya jaddada cewa karin kudin na da matukar muhimmanci don cimma muradun ma'aikatar, rahoton Leadership.

Manyan Najeriya ke daukar nauyin ta'addanci don hakar ma'adanai - Alake

A wani labarin na daban, ministan ma'adanai, Dele Alake ya yi ikirarin cewa manyan mutane ke daukar nauyin 'yan bindiga don samun damar hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Mr Alake ya ce gwamnati na iya bakin kokarinta don daukar matakan da za su dakile ire-iren wadannan bara gurbi daga mummunan nufinsu kan al'umma da tattalin ariziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel