Idan Aka Halatta Shigo da Shinkafa, Siminti da Sauransu, Farashi Zai Sauko Inji Bankin Duniya

Idan Aka Halatta Shigo da Shinkafa, Siminti da Sauransu, Farashi Zai Sauko Inji Bankin Duniya

  • Bankin duniya bai goyon bayan tsarin CBBN na haramta shigo da wasu kaya Najeriya daga kasashen ketare
  • Masanan sun fitar da rahoto da ya nuna cewa bada damar kawo kaya daga waje zai iya rage adadin talakawa
  • Binciken da bankin duniya ya gudanar ya nuna farashi za su sauka kadan idan har aka bude kofar kasuwanci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bankin duniya ya ce cire takunkumi wajen shigo da wasu kaya daga ketare da aka yi a Najeriya zai taimakawa tattalin arziki.

Bankin duniyan ya bayyana haka a rahoton NDU da ya fitar kan Najeriya a shekarar 2023 inda ya nuna an dawo da biyan tallafin fetur.

Bankin Duniya
Bola Tinubu da jami'in bankin Duniya Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarin ganin ta rage adadin talakawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya fasa kwai, ya fadi farashin da ya kamata a saida fetur a gidajen Mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna matakin da aka dauka na janye haramcin shigo da jerin wasu kaya daga waje zai ceto mutane miliyan 1.3 daga talauci.

Nairametrics ta ce bankin duniyan ya sanar da hakan ne a lokacin da majalisar tarayya ta ke so a dawo da takunkumin da CBN ya cire.

‘Yan majalisar wakilan tarayya suna ganin zai fi kyau a daina bari a shigo da duk wasu dangin kayayyakin da za a iya samarwa a kasar.

Rahoton ya nuna a sakamakon takunkumin shigo da shinkafa ne farashin buhu ya yi tashin da ya gagari jama’a duk da ana noma ta a gida.

"Hasashen bankin duniya ya nuna idan aka halatta shigo da kayan da aka hana, farashinsu zai karye da 4.7%.
Wannan zai yi sanadiyyar fito da mutane miliyan 1.3 (0.6% na daukacin al’umma) daga kangin talauci."

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya: "Kar ku kuskura ku kara jefa bam kan fararen hula"

- Bankin Duniya

Jihohin da za su fi amfana da tsarin

Idan aka bada damar kawo kaya daga ketare, jihohin Kaduna, Ekiti, Enugu, Kwara, Anambra da kuma Adamawa za su fi amfana sosai.

Bankin ya ce tasirin zai shafi Abuja, Kuros Ribas da Kebbi fiye da garuruwa irinsu Ribas, Akwa Ibom, Ondo, Abia, Imo, da kuma Ebonyi.

Yadda aka hana shigo da wasu kaya

Sabon gwamnan CBN ya rusa tsarin da aka yi wanda ya haramta bada kudin kasar waje domin shigo da kaya irinsu shinkafa, siminti da taki.

Masanan duniyan suna ganin hakan ya yi daidai domin zai taimakawa talakawa a Najeriya, sannan tsarin zai inganta walwalar al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel