Harin Bam a Kaduna: Mazauna Garin Tudun Biri Sun Karyata Kai Karar Gwamnatin Tinubu Kotu

Harin Bam a Kaduna: Mazauna Garin Tudun Biri Sun Karyata Kai Karar Gwamnatin Tinubu Kotu

  • A'ummar garin Tudun Biri, da sojoji suka yi sakarwa bama-bamai da ya kashe akalla mutum 100 sun musanya shigar da gwamnatin tarayya kara
  • A baya ne aka ruwaito wasu sun shigar da gwamnati kara a babbar kotu inda suke neman diyyar Naira biliyan 33 a madadin iyalan da aka kashe 'yan uwansu
  • Sai dai hakimin Ifira, Balarabe Garba, a ganawarsa da gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce ba su da masaniya kan shigar da wannan karar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Shugabannin mazauna garin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna sun nesanta kansu daga karar da aka shigar kan gwamnatin tarayya biyo bayan harin bam a garin.

Kara karanta wannan

Duk da jerin alkawura, 'yan Tudun Biri sun kai karar Gwamnati a Kotu ana neman N33bn

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da suka yi ikirarin 'yan garin ne suka kai karar gwamnatin tarayya, inda suka nemi diyyar Naira biliyan 33 kan mutunensu da aka kashe.

Mazauna garin Tudun Biri sun karyata kai karar Tinubu kotu
"Ba mu da hannu a karar da aka shigar kan gwamnatin tarayya", cewar mazauna garin Tudun Biri. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ba mu da hannu a shigar da gwamnati kara - Hakimin Ifara

Sai dai, hakimin Ifira, Balarabe Garba, wanda ya jagoranci wadanda abin ya shafa zuwa ga gwamnan jihar, Uba Sani a ranar Laraba, ya ce ba su da masaniyar shigar da karar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sun gamsu da irin kokarin da gwamnatin jihar da na tarayya suke yi kan su tun bayan faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Garba:

"Ba mu da hannu a karar da aka shigar kan gwamnatin tarayya. Mu 'yan kasane masu bin doka da oda, ba za mu bari wasu su yi amfani da mu don cimma manufarsu ba."

Kara karanta wannan

Dabara ta kare: 'Yan sanda sun kama shaharrun masu satar mota a jigawa

Martanin Gwamna Uba Sani kan shigar da karar

Rabaran Musa Saidu ya ce duk da garin ya kunshi Musulmai da Kirista, hakan bai hana su zaman lafiya tsawon shekaru ba, don haka ya ce ba za su bari a lalata wannan tarihin ba.

Gwamna Uba sani ya sha alwashin gano wadanda suka shigar da karar da sunan 'yan kauyen don jin ba'asi da bin kadi, a cewarsa hakan neman tayar da zaune tsaye ne, rahoton The Cable.

Gwamnan ya kuma ce duk wata gudunmowa da gwamnatin jiha da tarayya suka bayar za a mika su ga al'ummar garin nan ba da jimawa ba.

Mutumin garin Tudun Biri ya je Kotu

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani mutum mai suna Alhaji Dalhatu Salisu ya shigar da karar gwamnatin tarayya a kotu a madadin mazauna garin Tudun Biri.

Mukhtar Usman Esq, lauyan Salisu ya ce sun je kotun tarayyan ne saboda dokar kasa ta ba kowa damar rayuwa, amma sojoji su ka kashe jama’a haka kurum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel