Tinubu Na Cikin Iftila’i Yayin da Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin Zai Same Shi a 2024

Tinubu Na Cikin Iftila’i Yayin da Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin Zai Same Shi a 2024

  • Fitaccen Fasto a Najeriya ya yi wasu hasashe masu tayar da hankali a shekarar 2024 inda ya ce a dage da addu’a
  • Fasto Chris Ajabor ya ce ya hango Shugaba Tinubu ya fita neman lafiya kasar ketare inda ya ce dole a dage da addu’a
  • Faston ya kuma ce Sanata Adams Oshiomole na fuskantar barazana wanda ya ke bukatar addu’a sosai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shahararren Fasto a Najeriya, Chris Ajabor ya yi hasashen abin da zai faru da Shugaba Tinubu.

Chris ya ce Tinubu na cikin hatsarin kamuwa da mummunan rashin lafiya wacce za ta iya fitar da shi kasar ketare, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Idan aka halatta shigo da shinkafa, siminti da sauransu, farashinsu zai sauko – Bankin duniya

Malamin addini ya bukaci addu'a yayin da ya hango iftila'i ga Shugaba Tinubu
Fasto ya yi hasashen abin da zai faru da Tinubu a 2024. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane hasashe Faston ya yi a Najeriya kan Tinubu?

Faston ya ce Tinubu ya kusa mutuwa amma ubangiji ya taimake shi ya tsira daga iftila’in inda ya ce ya hango ana sauya masa jini a jiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci ‘yan kasar da su dage da addu’a don taimakon shugaban kasar da ke fuskantar barazana.

Ajabor ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook inda ya bukaci ‘yan Najeriya su dage da addu’a ga Sanata Adams Oshiomole don ya na cikin bala’i.

Wane hasashe Faston ya yi kan Oshiomole?

Ya kara da cewa ya hango Oshiomole an wuce da shi kasar Ingila don sauya masa wani bangare na jikinshi.

Malamin addinin ya kuma yi hasashen wasu muhimman abubuwa da za su faru a shekarar 2024.

Ajabor ya kuma ce akwai hasashen gudanar da mummunar zanga-zanga da za ta lakume rayukan mutane da dama.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 sun koka da kasafin kudin 2024, abin da Tinubu ya ware masu ya yi kadan

Jigon APC ya yi fadi abin da zai faru da Tinubu a 2027

A wani labarin, Jigon jam’iyar APC, Salihu Lukman ya gargadi Shugaba Tinubu kan irin mulkin da ya ke yi a kasar.

Lukman ya ce akwai barazana idan har ba a dauki matakai da za su rage wa jama’a halin kuncin da su ke ciki ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel