Majalisar dokokin tarayya
A yau Litinin 31 ga watan Yuli ne Majalisar Najeriya ta fara tantance wasu daga cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya tura sunayensu don nada su ministoci.
Dr. Mariya Mahmood Bunkure ta samu goyon bayan duka Sanatocin Jihar Kano a Majalisar Dattawa. Wannan likita ce ta canji Maryam Shetty a makon da ya gabata.
Zuwa yanzu an tantance kusan duka Ministocin. Mutum 2 su ka ragewa ‘Yan Majalisa, Sai ranar Litinin ne Festus Keyamo da Mariya Bunkure za su san makomarsu.
Hankalin Sanatocin da su ka fito daga Arewa bai kwanta da shiga yaki a Nijar ba, su na ganin babu dalilin ayi amfani da karfin tuwo idan akwai damar ayi sulhu
Hannatu Musa Musawa ta fashe da kuka da ta hallara a gaban Sanatoci domin tantance ta. Hawaye ya rika kwararowa 'Yar Musawar lokacin da ta je Majalisar a jiya.
Majalisar dattawa ta bayyana rashin jin dadinta da yadda 'yan faucen waya ke shiga majalisa suna sace wayoyin sanatoci ba gaira babu dalili haka siddan kawai.
A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli ne aka yi rabon kwamitoci a Majalisar Wakilan Najeriya ta 10. Wasu daga cikin 'yan Majalisun sun yi nasarar dawowa kwamitocin.
Akalla mata yan majalisar dokokin tarayya shida ne suke da nasaba da tsoffin gwamnoni da wasu fitattun yan siyasa. Suna da alaka na jini da kuma na auratayya.
Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin jihar uku bisa zarginsu da aikata almundahana a yayin gudanar da harkokin.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari