Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

  • Hawaye ya rika kwararowa Hannatu Musa Musawa a lokacin da ta je gaban ‘Yan Majalisar tarayya
  • Mai ba shugaban Najeriyar shawara ta na cikin wadanda aka tantance a matsayin Ministoci a jiya
  • Hannatu Musawa ba dauki wani dogon lokaci ba, Sanatoci su ka bada shawarar ayi na’am da ita

Abuja - Hannatu Musa Musawa ta fashe da kuka a yayin da ake kokarin tantance ta domin zama Minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bibiyi abin da ya faru a yammacin Talata a majalisa, an ga yadda Hannatu Musa Musawa ta yi kuka da ke gabatar da jawabi.

Da aka bukaci ta gabatar da kan ta, Musawa ta fara ne da neman tsari daga shaidanu, sannan sai ta kira sunan Allah madaukakin Sarki (SWT).

Tantance Ministoci
Bola Tinubu zai nada Hannatu Musawa Minista Hoto: Barrister Hannatu Musawa
Asali: Facebook

Kamar yadda wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya nuna, da Hadimar shugaban kasar ta shiga jawabi, sai da Godswill Akpabio ya tsaida ta.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hannatu Musawa ta dauko dogon labari

Shugaban majalisar dattawar ya nusar da Bakatsiniyar za ta yi takaitaccen bayani ne kan rayuwarta, ba tamkar jawabi a majalisar dinkin Duniya ba.

Premium Times ta ce Musawa ta fara ne daga labarin mahaifinta wanda ya tashi a matsayin talaka a garin Bichi da ke Kano, ya na mai saida goro.

Sannu a hankali wannan mutum ya hadu da Malam Aminu Kano a gwagwarmayar NEPU, hakan ya yi sanadiyyar zuwansa jami’a a kasar Amurka.

'Yar talaka za ta zama Minista

Samun ilmi ya canza rayuwar wannan Bawan Allah wanda shi ne Musa Musawa, mahaifin Hannatu Musawa da ke shirin zama Ministan tarayya.

Ganin mahaifinta ya rasu ba tare da ganin wannan rana ba, shi ya sa ‘yar siyasar ta rika hawaye.

A cewar Lauyar, Marigayi Musa Musawa wanda ya zama fitaccen ‘dan siyasa, ya taimaka musamman wajen ganin ‘ya ‘yansa sun yi ilmin boko.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Sanata Mai Fada a Ji? Hadimin Gwamna Ya Bayyana Gaskiyar Zance

Musawa ba ta amsa tambaya ba

Elisha Abbo ya kawo shawarar da Kawu Sumaila ya mara masa baya, ba ayi wa Musawa wata tambaya, mafi yawan Sanatoci su ka amince da ita.

Sanatocin sun ce hakan zai nuna majalisa ta na ganin darajar mata, musamman ganin Bola Tinubu ya zakulo mata har bakwai a jerin Ministocinsa.

Ragowar Ministoci za su fito

Labarin da mu ka samu shi ne watakila wasikar Bola Ahmed Tinubu game da karin sunayen Ministoci ta isa teburin shugaban Majalisar dattawa a yau.

Ana shirin tura sunayen sahu na biyu na mutanen da ake so su zama Ministoci daga Kano, Legas, Adamawa, Gombe da duk sauran jihohin da su ka rage.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel