Sanatoci Sun Dakatar Da Tantance Mutum 1 Da Ya Rage a Jerin Ministoci; Kai tsaye

Sanatoci Sun Dakatar Da Tantance Mutum 1 Da Ya Rage a Jerin Ministoci; Kai tsaye

FCT Abuja - Biyo bayan fitar da sunayen mutane 28 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaba don nada su minista a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, Majalisa za ta fara tantance su a yau Litinin, 31 ga watan Yuli.

Rahotanni sun nuna cewa mutane 15 cikin wadanda aka zaba don nada su minista, sun riga sun mika takardunsu ga ofishin Babban Mataimakin na Musamman ga Shugaba (Majalisa) kan Harkokin Majalisa, Abdullahi Gumel.

Kasance tare da Legit.ng Hausa domin samun bayanai kai tsaye dangane da tantance wadanda aka zaba don nada su ministocin.

A ranar Litinin dinnan ake sa ran a kammala tantance wadanda shugaban kasa ya zaba domin su rike mukaman ministocin tarayya.

An tantance Keyamo

An tantance Keyamo

A karshe dai majalisar dattawa ta tantace Festus Keyamo, inda kwararren Lauyan ya bada hakurin abin da ya yi a baya.

Tashar talabijin Channels TV ta fitar da wannan rahoto, ta ce tsohon Ministan ya bar majalisa.

Abin da ya kawo rigima shi ne yadda gwamnatin tarayya ta rabawa masu kananan karfi N52bn sa'ilin Keyamo ya na ofis.

Wannan karo ya yi wa Sanatoci bayanin yadda aka raba kudin, yake cewa sai da CBN su ka sa ido, ya ce bai taba sisin kobo ba.

Premium Times ta ce 'yan majalisar sun karbi afuwar da 'dan siyasar ya nema.

Akpabio ya dawo daga Villa

Bayan an yi ta kai-komo wajen tantance Festus Keyamo, shugaban majalisa ya dawo daga ziyarar da ake tunani ya kai zuwa Aso Rock.

Festus Keyamo

Da kimanin karfe 1:25, Festus Keyamo SAN ya shigo zauren majalisa domin a tantance shi, Godswill Akpabio ya fara da yabonsa.

Lauyan ya ce ya yi aiki da Godswill Akpabio SAN a lokacin ya na Ministan Neja-Delta, shi kuma ya na karamin Minista a ma'aiktar.

Premium Times ta ce Keyamo ya gabatar da kan shi, ya fadawa Sanatoci ya na shirin tafiya yawon shakatawa, ya ji za a ba shi minista.

NTA TV ta ce Sanata Darlington Nwokocha ya bada shawarar a duba abubuwan da Lauyan ya yi a lokacin da ya rike wannan mukami.

Festus Keyamo SAN ya gamu da cikas

Sanatan na Abia ya kafa hujja da sashe na 88 na tsarin mulki, ya na cewa Keyamo ya ki zuwa gabansu a sa’ilin da su ka gayyato shi a 2020.

Premium Times ta ce Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi na’am da batun, ya ce Lauyan ya yi wa Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai taurin-kai.

Dr Mariya Mahmoud Bunkure

An kira Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta bayyana a gaban majalisar dattawa domin a tantance ta kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Likitar ta fara bayani ne da cewa ta kammala digiri a ilmin likitanci daga jami'ar Bayero da ke garin Kano a 2005, tayi NYSC a Filato.

Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin ya ji dadin yadda Bola Tinubu ya zakulo Dr. Bunkure a Ministocinsa, ya na yabon 'yar jiharsa.

An rahoto Barau Jibrin ya na cewa wanda ake sa ran ta zama Minista ta taso ne daga gidan da babu hali, amma ta iya zama Likita a Kano.

Sanata Kawu Sumaila wanda yake wakiltar Bunkure a majalisar, ya ce mutanen Kudancin Kano sun ji dadin jin labarin bada sunanta.

Sanatoci:Osita Izunaso, Tony Nwoye da Dave Umahi sun yaba da Shugaban kasa ya dauko Mariya Bunkure, su ka shiga yi mata tambayoyi.

Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya ya nuna ya na goyon bayan wanda ke gabansu.

Mohammed Monguno da Darlington Nwokocha sun jefo tambayoyi a kan jarrabawar MDCN da batun darasin tarihi a makarantun Najeriya.

Bayan amsa duk wasu tambayoyi, an tantance Mariya Mahmoud Bunkure.

Za a cigaba da tantance Ministoci

Sanata Opeyemi Bamidele ya bada shawarar a cigaba da tantance ragowar mutanen da suka rage a jerin sunayen Ministocin da aka aiko.

Shugaban marasa rinjaye, Simon Mwadkwon ya goyi bayan bukatar Sanata Bamidele. Daga nan sai aka fara shirin cigaba da aiki.

Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya iso

Rahoton Premium Times ya ce Godswill Akpabio wanda shi ne Shugaban Majalisa ya hallara domin zaman da za ayi a yau Litinin 7 ga watan Agustan 2023.

An tantance mutane 26 cikin wadanda Shugaba Tinubu ya tura majalisa

Lateef Fagbemi SAN ya zama mutum na 26 da aka tantance a zauren majalisar bayan ya amsa tambayoyin da aka yi kan shari'a.

Farfesa Muhammad Ali Pate wanda aka haifa a 1968 shi ne na gaba da za a tantance, Tsohon Ministan kiwon lafiya ne a Najeriya.

Da yake amsa tambayoyi a kan harkar lafiya, Muhammad Ali Pate ya ce ba don nadin Minista ba, da gobe zai zama shugaban GAVI.

An tantance Lateef Fagbemi SAN

Mutum na uku da za a tantance a yau shi ne Lateef Fagbemi SAN, wanda ake so ya wakilci mutanen jihar Kwara a majalisar FEC.

Akwai yiwuwar Lauyan zai zama Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnati. Za a saurari takaitaccen bayani a game da shi.

Fagbemi ya nuna dole a gyara yadda EFCC da ICPC su ke binciken barayi, amma bai goyin bayan a barka ofishin Ministan shari'a.

Za a tantance Mohammed Idris a matsayin wanda Tinubu zai nada minista

Bayan kammala tantance Dele Alake, Legit.ng Hausa ta na sa ran za a tantance Mohammed Idris bayan tsawaita lokacin zaman yau.

Mohammed Idris Malagi ya na amsa tambayoyin da Sanatocin Neja,Bauchi, Benuwai da Ogun su ka jefa masa bayan ya gabatar da kan shi.

Kwararren ‘dan jaridan ya tabo yadda za a samar da ayyukan yi tare da karin haske a kan yadda ake kula da labarai da lasisin watsa labarai.

An gama tantance Malagi wanda ake sa ran zai wakilci Jihar Neja a Majalisar FEC.

Isowar Dele Alake

Channels ta ce wanda za a tantance a majalisar shi ne Dele Alake, wanda yanzu haka shi ne Mai magana da yawun shugaban kasa.

'Dan siyasar ya yi bayanin gwagwarmayar da ya yi bayan zaben MKO Abiola.

Wadanda su ka jefawa Alake tambayoyi sun hada da Muhammadu Sani Musa, Sahabi Ya'u, Abdul Ningi da Aminu Tambuwal.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Davou Mwadkwon ya bukaci Dele Alake ya karanto taken Najeriya watau ‘National Anthem’.

Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban masu rinjaye ya zargi Mwadkwon da kawo siyasa, Godswill Akpabio ya yi watsi da batun.

Bayan gama amsa tambayoyi da su ka shafi aikin jarida, kafofin sadarwa na zamani, harkar yawon bude ido, an ba Alake damar ya tafi.

Akpabio ya iso Majalisa

Tashar Channels TV ta wallafa bidiyon Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio yayin da ya hallara a zaren majalisa.

Sai gobe za a cigaba

A yau aka tantance Nasir El-Rufai, Dave Umahi, Olawale Edun, Uche Nnaji, Misis Stella Okotete da kuma Adebayo Adelabu.

Tashar Channels ta ce an tantance Ekperikpe Ekpo, Hannatu Musawa da Ahmad Musa Dangiwa.

Wadanda su ka rage su ne Dele Alake; Lateef Fagbemi; Muhammad Idris, Ali Pate da oris Uzoka, za a tantance idan an dawo ranar Laraba.

An tafi gajeren hutu

Majalisar dattawa ta tafi hutun minti 30 bayan shawarar da Sanata Opeyemi Bamidele ya kawo, sai 4:30 za a cigaba da tantance Ministocin.

Da aka dawo hutun ne aka tantance Uche Nnaji daga Enugu, wanda ya bada labarin rayuwarsa da manufofinsa a lokacin tana takarar Gwamna.

Ahmad Musa Dangiwa

Ahmad Musa Dangiwa ya fara gabatar da kan shi daga haihuwa a 1963 zuwa karatun digiri a Jami'ar ABU Zariya har ya fara aiki.

Sanatocin Katsina duk sun yi tarayya wajen yabawa Arch. Ahmad Musa Dangiwa.

Sanata Benson Friday Konbowei ya dauko maganar takardar shaidar harajin Dangiwa, ya zarge shi da kin biyan haraji.

Da karfe 3:50, aka gama yi masa tambayoyi, ya kuma kama hanyar gabansa.

Nasir El-Rufai ya shigo zauren Majalisa

Nasir Ahmad El-Rufai ya fara bayyana kan shi a matsayin wanda aka haifa a kauyen Daudawa a Katsina, ya kuma tashi a Kaduna.

Malam El-Rufai ya karanto makarantun da ya yi karatun ilmin shari'a, kasuwanci, komfuta a Zariya, kasar Amurka da wasu wurare.

Kamar yadda ya fada, an tantance shi ya zama Ministan Abuja a 2003 bayan ya rike BPE, daga nan ya shiga CPC har aka kafa APC.

Abdulaziz Yari ne ya fara yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna tambayoyi kan yadda zai bunkasa bangaren wutar lantarki.

Ibrahim Khalil ya ce Sanatocin Kaduna sun amince da tsohon Gwamnan, kuma tun da tsohon Minista ne, ba sai an yi masa tambaya ba.

Sanatan Kogi ta yamma ya yabi El-Rufai amma yana da korafi a kan shi, sai dai Sani Musa ya ce a kyale tsohon Gwamnan ya yi tafiyarsa.

El-Rufai ya amsa yadda zai gyara harkar wuta idan ya zama Minista, ya kawo matsalar karancin gas, siyasa da rashin kayan aiki.

Tsohon Ministan yana sa ran gwamnati mai-ci ta magance matsalar a shekara bakwai, kafin a iya yin wannan, ya ce sai an hada-kai.

An gama tantance El-Rufai ba tare da maida hankali kan ikirarin korafin a kan shi ba.

A wannan bidiyo da aka wallafa a Twitter, za a ga lokacin da Malam El-Rufai yake barin majalisar dattawa bayan an tantance shi dazu.

Adebayo Olawale Edun ya burge Goje

Adebayo Olawale Edun ya gabatar da takaitaccen tarihinsa da karatun zamani da fara aiki a kasar waje, har zuwa zamansa Kwamishina a Legas.

Masanin tattalin ya ce ya bada gudumuwa wajen bunkasa tattalin arzikin Legas a zamanin Bola Tinubu

A matsayinsa na Sanata daga jihar Ogun,Sanata Solomon Olamilekan Adeola ya bada shawarar a amince da Wale Edun a matsayin Ministan tarayya.

Kamar dai Sanata Aliyu Wadada, shi ma Mohammed Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta tsakiya ya yi masa tambayoyi bayan nuna goyon baya.

Gbenga Daniel ya ce saura kiris Edun ya zama Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, a cewarsa ya san shi tsawon shekaru 35 da suka wuce.

Mista Edun ya ce a lokacinsa an toshe hanyoyin wawurar kudi tare da kirkiro fasahohin zamani, an kawo tsare-tsaren da za su jawo ‘yan kasuwa.

A cewarsa, cire tallafin fetur da daidaita kudin waje zai bunkasa tattali.

Ali Ndume ya yi dogon kira ga wanda ake tantancewan, ya na mai nuna damuwarsa game da darajar Naira, kudin kasar waje da cire tallafin man fetur.

Ahmad Lawan ya nemi ta yadda za a rabawa talakawa kudi alhali ba su da akawun, shugaban majalisa ya karanto masa abin da tsarin mulki ya ce.

Amsarsa ta karshe kuwa ita ce shugaba Bola Tinubu ba zai yi abin da ya saba doka wajen taba dukiyar kasa ba, ya ce zai yi aiki da tsarin mulki.

David Umahi ya iso Majalisa

Wanda aka fara da shi a ranar Talata shi ne Sanata David Umahi wanda ‘dan majalisar dattawa ne da yake shirin zama Sanata.

Channels TV ta rahoto shi yana bayyana kan shi ta hanyar jero ayyukan da ya yi a matsayin shugaban APC zuwa Gwamna da Majalisa.

‘Dan siyasar ya yabi majalisa a karkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio wanda ya ce ya rike Sanatoci ba tare da sabani ba.

Ba ayi wata-wata ba, Majalisar dattawa ta ba Umahi dama ya yi gaisuwar tantancewa.

Badaru Abubakar Bai Gamu Da Tsauraran Tambayoyi Ba Yayin Tantance Shi A Majalisa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar na cikin wadanda majalisa ta tantance a yau Litinin.

Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya ce akwai kyakyawan alaka tsakaninsa da tsohon gwamnan don haka ya umurci ya wuce ba tare da an masa wasu tsauraran tambayoyi ba, rahoton BBC Hausa.

Majalisar na tantance mutanen da Shugaba Tinubu ya tura sunayensu ne don neman amincewarta kafin nada su ministoci a ma'aikatu daban-daban.

Majalisa Ta Tantance Abubakar Kyari a Matsayin Minista

Majalisar Tarayyar Najeriya ta tantance Sanata Abubakar Kyari a matsayin minista a gwamnatin Shugaba Tinubu, BBC Hausa ta rahoto.

Kyari dan asalin jihar Borno ne kuma shine shugaban riko na jam'iyyar ta APC mai mulki a kasa.

Wanda aka fara tantancewa a yau shine Abubakar Momoh daga jihar Edo.

Kyari bai sha tsauraran tambayoyi ba saboda kasancewarsa tsohon dan majalisa dattawa.

Sunayen Ministoci: Majalisa Ta Fara Zaman Sauraron Tabbatar Da Zababbun Ministoci 16

A kalla mutane 16 ne cikin wadanda Shugaba Bola Tinubu ya zaba za a tabbatar da su a yau.

Ga sunayensu:

Sen.Abubakar S.Kyari - Borno

2. Abubakar Eshiokpekha Momoh - Edo

3. Nyesom Ezenwo Wike - Rivers State

4. Engr. Prof. Joseph Terlumun Utsev - Benue

5. Sen. John Owan Enoh - Cross River

6. Hon.(Bar) Bello Muhammad - Sokoto

7. Mohammed Badaru Abubakar -Jigawa

8. Amb.Yusuf Maitama Tuggar- Bauchi

9. Sen. Abubakar Sani Danladi -Taraba

10. Barr. Uju-Ken Ohaneye - Anambra

11. Hon. (Dr). Olubunmi Tunji-Ojo - Ondo

12. Dr. Betta Edu - Cross River

13. Iman Sulaiman Ibrahim - Nasarawa

14. Arch. Ahmed Musa Dangiwa - Katsina

15. Chief Uche Geoffrey Nnaji - Enugu

16. Stella Erhuvwuoghene Okotete - Delta

Ministocin Tinubu: Wike Ya Iso Majalisar Tarayya Domin Tantancewa, Bidiyo Ya Fito

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya iso Majalisar Tarayya domin tantance shi a matsayin minista.

Sunan Wike na cikin jerin sunayen mutane 28 da Shugaba Bola Tinubu zai nada minista da aka fitar a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli.

A wani bidiyo da Legit.ng ta yi karo da shi, an hangi Wike sanye da kwat hadimansa na masa rakiya zuwa cikin harabar majalisar tare da jami'an tsaro.

Zababbun Ministoci: Majalisa za ta tantance El-Rufai, Wike, Badaru, Adelabu da saura

FCT Abuja - Majalisa tana shiri don tantance da tabbatar da mutanen da Shugaba Tinubu ya zaba don nada su ministoci.

Shahararrun sunaye cikinsu sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi da wasu.

Ga jerin sunayen wadanda aka zaba din daga jihohi da shiyoyi.

Kudu maso Kudu

Nyesom Wike – Rivers

Abubakar Momoh – Edo

Betta Edu – Cross River

Ekperikpe Ekpo – Akwa Ibom

Stella Okotette – Delta

John Enoh – Cross River

Kudu maso Yamma

Olubunmi Tunji Ojo – Ondo

Dele Alake – Ekiti

Olawale Edun – Ogun

Waheed Adebayo Adelabu – Oyo

Kudu maso Gabas

Uche Nnaji – Enugu

Doris Aniche Uzoka – Imo

David Umahi – Ebonyi

Nkeiruka Onyejocha – Abia

Uju Kennedy Ohaneye – Anambra

Arewa maso Gabas

Yusuf Maitama Tuggar – Bauchi

Ali Pate – Bauchi

Abubakar Kyari – Borno

Sani Abubakar Danladi – Taraba

Arewa maso Yamma

Badaru Abubakar – Jigawa

Nasiru Ahmed El-Rufai – Kaduna

Ahmed Dangiwa – Katsina

Hannatu Musawa – Katsina

Bello Muhammad Goronyo – Sokoto

Arewa maso Tsakiya

Lateef Fagbemi – Kwara

Muhammad Idris – Niger

Iman Suleiman Ibrahim – Nasarawa

Joseph Utsev – Benue

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164