A Duba Dai: Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki Da Kasar Nijar Ba

A Duba Dai: Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki Da Kasar Nijar Ba

  • Sanatocin da su ka fito daga mazabun yankin Arewa su na da ja game da shiga yaki da kasar Nijar
  • Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya bayyana matsayar su a karkashin jagorancin Abdul Ningi
  • ‘Yan majalisar su na ganin babu dalilin ayi amfani da karfin tuwo idan dai akwai damar ayi sulhu

Abuja - Sanatocin da su ka fito daga jihohin Arewacin Najeriya, ba su gamsu da maganar daukar makami a kan sojojin Jamhuriyyar Nijar ba.

Shugabannin kungiyar ECOWAS su na neman yakar Nijar a sakamakon juyin mulki da sojoji su ka yi, Tribune ta ce wasu Sanatoci su na da ja a kai.

Wakilan jihohin Arewa a majalisar dattawa, sun fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa ya sake nazari kan maganar shiga Nijar da yaki.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Murkushe Arewa Tun Wajen Nada Ministoci

Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya yana so a yaki Nijar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sulhu alheri ne

Daily Trust ta ce ‘yan majalisar Arewa a karkashin Abdul Ningi su na ganin ba matakin da ya dace a dauka shi ne yin sulhu da sojojin tawayen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila wanda shi ne Mai magana da yawun bakin Sanatocin Arewa a majalisar dattawa, ya fitar da jawabi.

Da yake magana ranar Juma’a a Abuja, Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce matsayarsu ita ce a bi matakin siyasa a wajen magance rikicin.

Jawabin Abdulrahman Kawu Sumaila

“Ba mu goyon bayan a kai ga amfani da karfin bindiga sai dai idan an yi amfani da duk matakan da aka ambata
Dalili kuwa saboda irin abin da zai biyo baya na kashe-kashen ‘yan kasar da ba su da laifin komai.
Baya ga haka, kusan jihohin Arewa bakwai su ka yi iyaka da Nijar, su ne: Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno, abin zai shafe su.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Gonan Sanata a Arewa, An Rasa Rai

Mu na kuma sane da halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da Libya, wanda zai iya shafan wadannan jihohin Arewan, idan aka yi amfani da soji.

- Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila

Sumaila ya ba abokan aikinsa shahara su yi hattara wajen amfani da sashe na 5 na karamin sashen (4) (a) da (b) a kundin tsarin mulki da ya halatta yaki.

Takardar shugaban kasar ta je Majalisa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikowa majalisar dattawa takardar neman izinin tura dakaru zuwa makwabta a karkashin kungiyar ECOWAS.

A haka aka rahoto Shehu Sani wanda ya je majalisa tsakanin 2015 da 2019 ya na ba Sanatoci shawara su duba abin da zai biyo bayan yakar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel