Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai

Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai

  • Rashin tabbatar da tsohon gwamna Nasir El-Rufai a matsayin ministan Najeriya na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin manyan yan kasar
  • A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta, majalisar dattawa ta sanar da cewar ba a tabbatar da El-Rufai da wasu zababbin ministoci ba saboda ana jiran rahotannin tsaro
  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce maimakon hana tsohon gwamnan Kadunan mukamin minista, kamata ya yi majalisar ta sa shi rantsuwa kafin tabbatar da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon babban mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan kafofin watsa labarai, Doyin Okupe ya bukaci mjalisar dattawa da ta sake duba matsayinta kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

El-Rufai na cikin zababbun ministoci 48 na shugaban kasa Bola Tinubu. Sai dai kuma, majalisar dattawan ta ki tabbatar da shi a matsayin minista.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da El-Rufai Da Wike a Gidan Gwamnati

Doyin Okupe ya roki majalisa da ta tantance El-Rufai
Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai, Nigerian Senate
Asali: Facebook

El-Rufa'i zai zama ma'aikatar wutar lantarki?

A cewar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, majalisar ba ta wanke El-Rufai ba saboda rahotannin tsaro da dole sai an magance.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake martani a kan ci gaban, Okupe ya ce, "mutane kadan ne za su yi shakkar cancantar El-Rufai da kuma gagarumin aikin da zai iya yi" - don haka ya kamata 'yan majalisar su sake tunani a kan hukuncinsu.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter:

“Ya kamata Majalisar Dattawan Najeriya ta sake duba matakin da ta dauka na cire tsohon Gwamna El Rufa’i daga cikin jerin Ministoci, ni ba masoyin Malam El Rufa’i ba ne wanda nake kallo a matsayin mai tsattsauran ra’ayi wanda a baya ya nuna wasu halaye na tsatsauran ra’ayi na yan rikau a addini.

Kara karanta wannan

MURIC Ta Nemi Bahasi Kan Kin Amincewa Da El-Rufai Mukamin Minista Da Majalisa Ta Yi, Ta Bayyana Dalili

"Duk da haka, mutane kalilan ne za su yi shakkar cancantar El Rufa'i da aikin da zai iya yi. Idan har da gaske ne ana tunanin basa ma'aikatar wutar lantarki, to ina ganin bai kamata mu yanke hancin mu ko fuskarmu don zub da yawu ba.
“Majalisar Dattawa za ta iya dagewa kan samun rantsuwa daga bangarensa kafin a tabbatar da shi cewa a lokacin da yake rike da mukamin minista, ba zai yi wani tsokaci ko martani kan addini ba.
"Ma'aikatar wutar lantarki na da matukar muhimmanci a tattalin arzikinmu da kuma kokarinmu na yaki da talauci."

Tinubu Na Ganawa Da El-Rufai Da Wike a Fadar Gwamnatin Tarayya

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya shiga gani da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Jaridar Vanguard ta ce bayan El-Rufai a wajen ganin, akwai tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng