Ministoci: Sanatoci sun Tantance Mutum 46, Binciken Jami’an Tsaro Ya Tsaida Ragowar 2

Ministoci: Sanatoci sun Tantance Mutum 46, Binciken Jami’an Tsaro Ya Tsaida Ragowar 2

  • Zuwa yanzu an tantance kusan duka sunayen da ke cikin jerin Ministocin da Bola Tinubu ya aiko
  • Mutum biyu rak su ka ragewa ‘Yan Majalisar Dattawa, sai ranar Litinin za a cigaba da tantance su
  • A cikin mutane 46, wadanda su ka rage su ne Festus Keyamo SAN da Mariya Mahmud Bunkure

Abuja - Majalisar dattawa ta daga tantance ragowar wadanda ake so su zama Ministocin Najeriya zuwa ranar Litinin, 7 ga watan Agusta 2023.

The Cable ta ce a ranar Asabar aka tantace Lola John, Ishak Salako, Bosun Tijani, Uba Ahmadu da Farfesa Tahir Mamman SAN a Majalisar dattawa.

Zuwa yanzu an tantace mutane 46 da sunayensu ya shiga hannun ‘yan majalisar, wadanda su ka rage su ne Festus Keyamo da Mariya Bunkure.

Sanatoci Ministoci
Sanatoci su na tantance Ministoci Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Za a cigaba a mako mai zuwa

Kara karanta wannan

A Duba Dai: Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki Da Kasar Nijar Ba

Kamar yadda ya saba, Sanata Opeyemi Bamidele wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya bukaci a janye zaman sai Litinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Opeyemi Bamidele, sai daga baya aka aiko da ragowar sunayen na mutum biyu, zuwa yanzu jami’an tsaro ba su gama bincike a kan su ba.

“Wasikar da ta aiko sunayen mutane biyu ta zo ne a makare kuma su na kan tattara takardunsu. Mu na jiran rahoton binciken jami’an tsaro.”
Ko zan bada shawarar mu jinkirta zaman tabbatar da su zuwa ranar Litinin da za a sake zaunawa.

- Opeyemi Bamidele

Sanatan Filato ta Arewa, Simon Mwadkwon ya goyi bayan takwaransa daga Ekiti. Ba zai yiwu majalisa ta zauna a yau ba saboda zuwa coci a yau.

Za a shiga ofis a Agusta

Punch ta ce akwai yiwuwar Ministocin da aka tabbatar su shiga ofis a mako na uku na Agusta.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Murkushe Arewa Tun Wajen Nada Ministoci

Ana sa ran tsakanin 14 zuwa 18 ga watan nan, Mai girma Bola Tinubu zai rantsar da Ministocin, kuma ya tura su zuwa ma’aikatun da za su yi aiki.

Ganin ranar Laraba ne ake yi zaman majalisar zartarwa, watakila Ministocin su hadu da juna a karon farko nan da kwana 10, a ranar 16 ga Agusta.

An sake aiko sunaye biyu

Kun ji labari Festus Keyamo tsohon karamin Minista ne da zai wakilci Delta, Mariya Bunkure ita ce wanda ta canji Maryam Shetty daga jihar Kano.

Hakan ya fusata wasu mabiya Twitter, akwai wadanda su ke ganin Maryam Shetty ta fi Bello Matawalle cancanta da zama Minista a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng