Yan ta'adda
Ana zargin ‘Yan Boko Haram sun gamu da fadan da ya fi karfinsu a lokacin da suka fashi. Sabani ya shiga tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Koma Kashe Kansu.
Ashirin da uku daga cikin fasinjojin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna hannun 'yan ta'adda bayan kwanaki 186 da sace su. An ce basu ji daga wurinsu.
Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Forest Sanity sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa tare da ceto wasu mutum 10 a samamen da suka kai maboyarsu.
A ranar Litinin, Sanata Ifeanyi Ubah ya tabbatar da mutuwar wasu daga cikin hadimansa da masu tsaron lafiyarsa a yayin wani farmaki da aka kai wa tawagarsa.
Wata kungiyar hadinn guiwa ta farar hula dake tabbatar da tsaro a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ta dakile farmakin 'yan ta'adda a garin Batsari.
Alamun da suka bayyana a cikin kwanakin karshen makon nan shi ne, ta yuwu a gurfanar da mai sasanci da 'yan bindiga, Tukur Mamu, kotu a Abuja ranar Litinin.
Hukumar sojojin Najeriya ta bayyana cewa har yanzu akwai sauran yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno guda 98 tsare a hannun yan ta’addan Boko Haram.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara sun yi nasarar kama wani mai suna Isiyaku Babangida, kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo.
Hedkwatar tsaro a ranar Alhamis ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun cafke mai kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a yankin Asokoro dake FCT, Abuja.
Yan ta'adda
Samu kari