Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki

Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki

  • Miyagun 'yan bindiga sun kutsa garin Jere dake kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka bindige ango Auwal wanda aka fi sani da Danlami
  • Auwal na tsaka da jinyar amaryarsa Rabiatu mai ciki, yayin da miyagun suka bayyana tare da yunkurin tafiya da ita, amma jarumin ya hana
  • Lamarin ya fusata 'yan bindigan inda suka harbe shi a hannu, amma ya ki bari su tafi da ita, hakan yasa suka yi masa harbi uku a ciki

Jere, Kaduna - A ranar da al'amarin zai faru, Auwal ya dauka amaryarsa Rabiatu inda ya kai ta dakin haihuwa dake Kwatas din Masukwani saboda laulayin ciki da take fama da shi.

Zuwa bayan isha'i duk a ranar, 'dan uwansa Rabi'u ya ziyarcesa tare da matarsa Aisha. Sun dade suna tattaunawa a kan rayuwa har sai da Rabi'u yace za su koma gida da matarsa.

Kara karanta wannan

Bayelsa: Fusatattun Matasa Sun Kona Wani Da Ake Zargi Da Sata

Hoton Auwal da Matarsa Rabi'atu
Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Ba su dade da tafiya ba inda suka bar Auwal kwance a kan tabarma yayin da amaryarsa ke kwance kusa da shi, kawai 'yan bindiga suka bayyana tare da zagaye gidan. Ba su yi harbi ba a kofar shiga saboda dare bai yi sosai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun bai wa Auwal umarni amma yayi shiru, a lokacin da suka fusata sai suka ce zasu tafi da Auwal tare da matarsa. Nan kuwa Auwal yace babu inda zasu je. Ya tashi ya rufe hanyar shiga dakin amma cike da rashin sa'a suka harbesa a hannu, Leadership ta ruwaito.

Mummunan harbin ya ragargaza kasusuwan hannun Auwal. 'Yan bindigan sun yi yunkurin daukar matar Auwal amma ya hana inda yace babu inda zasu je. A take suka harbe shi sau uku a ciki kuma ya fadi cikin jini. Bayan nan suka tafi da matar Auwal.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

'Dan uwan Auwal, Barde, yana cikin dakinsa yayin da lamarin ke faruwa amma ba shi da kwarin guiwar fitowa har sai da ya fahimci 'yan bindigan sun fice. A nan ya dinga ihu yana cewa sun kashe Danlami (Auwal).

Duk da halin da Auwal ke ciki, an ji yana cewa

"Ku dauke ni, sun tafi da matata" har ta kai ga baya iya cewa komai.

Wani makusancin Auwal ne ya bada labarin yadda 'yan bindiga suka kutsa garin Jere dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka kashe ango tare da yin a won gaba da matarsa mai tsohon ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel