Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

  • Jama'a mazauna wasu yankunan karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna sun fada tashin hankali bayan wucewar jirgin sama sannan 'yan ta'adda suka far musu a kasa
  • Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim, ya sanar da yadda ya fada kogi bayan ya ga wucewar jirgin saman wurin karfe 6 na yamma kuma a take 'yan ta'adda suka fara harbi
  • Sun halaka mutum 32 kamar yadda shugabannin Adara a yankin suka sanar, biyu kacal daga cikin mamatan ne mata, sauran duk maza ne

Kaduna - Joshua ya karba bakuncin wasu daga cikin mutanen da harin 5 ga watan Yuni ya ritsa da su. Sun nemi mafaka a gidansa dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Ya bayyanawa HumAngle cewa, da farko sun yi tsammanin cewa maharansu na samun taimako daga jirgin sama ne amma daga bisani sun gane cewa wucewa kawai yayi da dare ba tare da ya kashe kowa ba. Wannan bayanin ya yi daidai da bayanin wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim, wanda yace jirgin saman bai kashe kowa ba.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

'Yan Bindiga Dauke da Miyagun Makamai
Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Mun fara gudu. Ya wuce ta saman Unguwan Maikori. Amma bai halaka kowa ba," Ibrahim daga kauyen Bante yace kafin ya yi bayanin yadda ya tsira da ransa.
"Kogi na fada lokacin da jirgin saman ya zo. Za ka yi tunanin sojoji ne," yake bayani kan 'yan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan ta'adda dauke da bindigogi suka bayyana a yankin tare da fatattakar jama'a da ke wuraren Dogon Noma da Unguwan Mai Yashi.
"Bayan jirgin ya yi shawagi, wadanda ke kasan sun fara harbin mutane wurin karfe 6 na yamma, har yanzu ba a ga wasu ba. Da farko mutane 20 ne suka rasa rayukansu," Amana yace.

Amma shugabannin Adara a karamar hukumar sun ce mutum 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da suka ce jirgin sama ne ya taimakawa 'yan ta'addan.

Wasu daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su, sun dinga gudu cikin daren kuma sun isa Maraban Kajuru da safiyar Litinin, 6 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun yi Garkuwa da Mata 2 a Konduga, Kwamishinan 'Yan Sanda

A wannan ranar, 'yan ta'adda sun bayyana a babura kuma sun kone coci biyu a Unguwan Maikori da Dogon Noma.

"Sun shiga gidaje tare da sace kadarori da suka hada da tufafi. Da yawa daga cikin wadanda suka kashe maza ne, biyu daga cikin 32 kacal ne mata," Joshua, wanda kanin shi ya sha da kyar ya sanar.

Bayan mazauna yankin sun ji karar jirgin saman, sun ji tsoron rasa rayukansu bayan sun gane cewa ba dauki ya kawo musu ba.

Legit.ng tana kokarin samun kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige domin samun karin bayani daga gare shi.

Borno: Boko Haram Sun yi Garkuwa da Mata 2 a Konduga, Kwamishinan 'Yan Sanda

A wani labari na daban, Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, Abdu Umar, ya ce mayakan ta'addancin Boko Haram sun sace mata biyu a kauyen Mairari da ke karamar hukumar Konduga ta jihar.

Kara karanta wannan

Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

Umar ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri. Ya ce lamarin ya faru a ranar 7 ga watan Yuni.

"Wurin karfe 7:30, wani Ari Mustapha daga kauyen Mairari a Konduga ya kawo rahoton cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kutsa garinsu tare da sace 'ya'yansa biyu.
"Ya ce shekarunsu 26 da 30. Ya kara da cewa 'yan ta'addan sun sace masa shanu biyu da wasu kayansa kafin su tsere," kwamishinan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel