Da Dumi-Ɗumi: Fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'adda suka sako sun dira Abuja

Da Dumi-Ɗumi: Fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'adda suka sako sun dira Abuja

  • An kai Fasinjoji 11 da yan bindiga suka yarda suka saki birnin tarayya Abuja don cigaba da kula da su
  • Bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta yi musayar mutum 11 da ƴaƴansa yan ta'adda Takwas
  • Tukur Mamu, wanda ya shiga ya fita don tabbatar da wannan nasara, ya ce kamata ya yi a jinjina wa Buhari

Abuja - Mutane 11 daga cikin Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da aka sace, waɗan da yan ta'adda suka sako sun isa babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda mawallafin Desert Herald, Tukur Mamu, ya shiga ya fita har aka yi nasarar kuɓutar da mutanen waɗan da suka shafe kwanaki 70 a tsare.

Bayanai sun nuna cewa Fasinjoji 11 sun kubuta ne bayan tura wa yan ta'addan ƴaƴan su guda Takwas ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Insha Allahu zamu kubutar da duk mutanen da aka sace, da yuwuwar mu sake rufe layukan waya, Gwamnan Arewa

Cikin jirgin kasan da aka farmaka.
Da Dumi-Ɗumi: Fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'ada suka sako sun dira Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa maimakon yan ta'addan su sako baki ɗaya matan da ke hannun su kamar yadda aka yi yarjejeniya, sai suka sako mata Shida masu matsakaicin ƙarfi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika yan bindigan sun sako maza guda biyar waɗan da ke fama da rashin lafiya, jumulla dai sun saki mutum 11 kenan.

Majiyar ta ƙara da cewa ana tsammanin za'a haɗa mutanen da Allah ya cece su daga ƙangin garkuwa da iyalansu a can birnin tarayya wato Abuja.

Sunayen Fasinjojin da suka kuɓuta

Sunayen mutanen da yan ta'addan suka sako su ne; Amina Ba'aba Muhammad, Rashida Yusuf Busari, Amina Jibrin, Hanan Adewole, Najib Muhammad Ɗahiru, Hassan Aliyu, Peace A Boy, Ɗanjuma Sa'idu da kuma Gaius Sambo.

Mamu ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhati, shugaban ma'aikatan tsaro da sauran hukumomin tsaro ya dace a jinjina wa kan kokarin da suka yi kafin samun wannan nasara.

Kara karanta wannan

Yadda wasu ma’aikatan gidan gona a Abuja suka kashe ubangidansu, suka jefa gawarsa a cikin rijiya

Legit.ng Hausa ta zanta da wanu da yar uwarsa ke cikin waɗan da maharan suka tattara a harin jirgin kasan Kaduna-Abuja, ya ce har yanzun hankalin su ba'a kwance ya ke ba.

A cewarsa, sako mutum 11 labari ne mai daɗi duk da yar uwarsa ba ta ciki, amma idan ka duba adadin bai faka kara ya karya ba cikin yawan fasinjojin da ke tsare.

"Muna bukatar a taimaka mana da addu'a, gwamnati na kokari amma sai ta kara zage dantse, mu kaɗai muka san halin da muke ciki."

A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya

Wasu miyagun yan bindiga sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun aikata babbar ɓarna.

Bayanai sun nuna cewa m a haran sun sace shugaban matasan yankin, yayin da suka haɗa da Motoci masu tsada.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji da CJTF sun halaka dandanzon yan ta'adda, sun lalata kasuwa da sansanin su a Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel