'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyensu Sanata Abba, sun halaka mutum 15, wasu sun bace

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyensu Sanata Abba, sun halaka mutum 15, wasu sun bace

  • 'Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kutsa kauyen Igama dake Edumoga a jihar Benue inda suka yi ruwan wuta
  • Miyagun sun halaka a kalla mutum 15 yayin da wasu da yawa suka bace sannan suka kurmushe gidaje masu yawa a yankin
  • Mummunan lamarin ya faru ne yayin da jama'a ke haramar tafiya coci da safiyar Lahadi a karamar hukumar Okpokwu ta jihar Benue

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benue - Kusan mutum 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka bace a safiyar Lahadi bayan wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki kauyen Igama a Edumoga Ehaje, yankinsu Sanata Abba Moro a karamar hukumar Okpokwu ta jihar Benue.

Vanguard ta ruwaito cewa, an tattaro daga majiya cewa, maharan da suka kai harin sun bayyana da yawansu kuma sun kone gidaje a yankin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyensu Sanata Abba, sun halaka mutum 15, wasu sun bace
'Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyensu Sanata Abba, sun halaka mutum 15, wasu sun bace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Sun kutsa Igama da safe lokacin da mutane ke shirin tafiya coci a ranar Lahadi. Sun bayyana dauke da makamai kuma duk wanda suka ci karo da shi kashe shi kawai suka yi.
"Duk da ba za mu iya cewa ga yawan mutanen da suka halaka ba saboda har yanzu ba a gama samo gawawwaki ba, amma daga bayanin da muka samu, an halaka mutum 15 yayin da wasu har yanzu ba a gansu ba. An ga gawawwaki tara a yanzu amma ana cigaba da neman sauran," yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da aka tuntubi shugaban karamar hukumar, Amina Audu, ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace babu dalilin harin.

Shugabar karamar hukumar wacce tace ta je ofishin 'yan sandan Okpoga domin duba gawawwakin wadanda aka halaka, ta ce an kai gawa tara ma'adanar gawawwaki yayin da ake cigaba da neman sauran, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 74, an sako mutum 11 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Audu, wacce ta koka kan harin, ta sanar da cewa makiyaya dauke da makamai ne suka shiga yankin da yawansu.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce har a lokacin bata samu cikakken bayani daga 'yan sandan da suka je kauyen ba don ba su riga sun dawo ba.

Buratai: Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya

A wani labari na daban, Jakadar Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanat Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya bayyana hanyoyin da za a bi don kawo karshen rashin tsaro, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka don kawo tsaro.

Buratai, tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, ya yi magana a ranar Asabar a wani taron tsaro da aka yi na rana daya Arewa House a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel