Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra

  • Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Anambra inda suka kashe wani shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi
  • Miyagun sun kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Anambra Wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi, a jihar Anambra.

An tattaro cewa an kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra
Abun bakin ciki: Yan bindiga sun kashe wani dan siyasa a jihar Anambra Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa an sace shugaban matasan ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki gidansa da ke garin Ukpor.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun yi gaba da kusan miliyan N50m a Sakatariyar karamar hukuma

An tsinci gawarsa ne a wata mararraba da ke Utuh, yan kilomita kadan daga Ukpor, inda aka sace shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:

“Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun rigada sun cire gawar kafin jami’anmu su isa wajen.

“Binciken da jami’anmu suka zurfafa daga wasu shaidu a yankin, ya bayyana mutumin a matsayin wani Emeka Alaehobi wanda aka sace a ranar 9/6/2022 daga gidansa da ke Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta kudu.”

Kakakin yan sandan ya ce jami’ansu na bibiyar maharani, inda ya kara da cewa wadanda suka aikata ta’asar za su fuskanci shari’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel