'Yan Bindiga Sun Sheke Ado Mamman, Makiyayi a Kwali Dake Abuja

'Yan Bindiga Sun Sheke Ado Mamman, Makiyayi a Kwali Dake Abuja

  • 'Yan bindiga sun kutsa garin Pai da ke karamar hukumar Kwali ta babban birnin tarayya inda suka halaka Ado Mamman
  • Miyagun sun shiga Pai wurin karfe 11:12 na daren Lahadi kuma sun yi yunkurin sace mutane amma makiyayi Ado Mamman ya hana su
  • Fusatar da suka yi ce ta sa suka harbe shi har lahira tare da yin garkuwa da Maude Ado, Miyetti Allah ta tabbatar da faruwar lamarin

Kwali, Abuja - 'Yan bindiga sun halaka wani makiyayi mai suna Ado Mamman a wani yankin na Pai dake karamar hukumar Kwali ta Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mazaunin Pai wanda ya bayyana sunansa da Shehu, yace lamarin ya faru wurin karfe 11:12 na daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

'Yan Bindiga Sun Halak Ado Mamman
'Yan Bindiga Sun Sheke Ado Mamman, Makiyayi a Kwali Dake Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yace 'yan bindigan dauke da miyagun makamai sun kutsa yankin Fulanin yayin da suke kokarin kwanciya bacci.

Yace mamacin makiyayin an harbe shi a kirji yayin da yake kokarin hana su tafiya da mutanensa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Harbe-harben da suka dinga yi ne ya janyo hankalin mazauna kauyen, har zuwa karfe 4 na safiyar yau ne aka gane cewa 'yan bindigan sun halaka makiyaya tare da yin a won gaba da mutum daya," yace.

Makiyayin da aka sace sunansa Maude Ado.

Sakataren Kungiyar Makiyayan Miyetti Allah na Gwagwalada, Mohammed Usman, ya tabbatar da kisan tare da sace makiyayin a Pai.

Usman, wanda yace ya samu labarin wurin karfe 6:12 na safiyar Litinin, ya kara da cewa an birne mamacin.

"Amma a yanzu da muke magana, ba a riga an ji daga bakin wadanda suka sace Maude ba," yace.

Kara karanta wannan

Mutane 5 sun mutu yayinda aka yi karo tsakanin yan IPOB da wata kungiyar hamayya a Anambra

Kakakin Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine bata yi martani kan sakon kar ta kwana da aka tura mata kan lamarin.

Yadda Ango Ya Sheka Barzahu a Kokarin Hana 'Yan Bindiga Sace Matarsa Mai Ciki

A wani labari na daban, a ranar da al'amarin zai faru, Auwal ya dauka amaryarsa Rabiatu inda ya kai ta dakin haihuwa dake Kwatas din Masukwani saboda laulayin ciki da take fama da shi.

Zuwa bayan isha'i duk a ranar, 'dan uwansa Rabi'u ya ziyarcesa tare da matarsa Aisha. Sun dade suna tattaunawa a kan rayuwa har sai da Rabi'u yace za su koma gida da matarsa.

Ba su dade da tafiya ba inda suka bar Auwal kwance a kan tabarma yayin da amaryarsa ke kwance kusa da shi, kawai 'yan bindiga suka bayyana tare da zagaye gidan. Ba su yi harbi ba a kofar shiga saboda dare bai yi sosai ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku: 'Zunuban' Wike, Dalilan Da Yasa Aka Zabi Okowa, Majiya Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng