Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

  • Tawagar jami'an tsaro sun ceto maniyyatan hajjin bana daga hannu 'yan bindiga bayan wasu awanni da yin garkuwa dasu a Sokoto
  • An yi garkuwa da maniyyatan ne daga karamar hukumar Isa tare da 'yan uwansu da jami'an tsaron da suke musu rakiya zuwa sansanin mahajjatan
  • An ceto su cikin koshin lafiya sannan ana kokarin ganin sun tafi kasa mai tsarkin don yin aikin Hajji cikin kwanciyar hankali

Sokoto - An ceto maniyyatan hajjin bana na jihar Sakkwoto bayan sun dauki awanni a hannun 'yan bindigan da suka yi garkuwa dasu a sa'o'in farko na ranar Talata, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da gwamnatin jiha ta fitar wanda mai bada shawara ta musamman a lamurran da suka shafi yanar gizo Bello Muhammad ya bayyanawa manema labaran jihar Sakkwoto, an ceto maniyyatan hajjin banan cikin koshin lafiya ba tare da wani abu ya samesu ba.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Maniyyatan hajjin bana sun kai su 21 wandanda ke kan hanyarsu zuwa Sakkwoto, daga karamar hukumar Isa zuwa babban birnin jihar don su hau jirgin zuwa masarautar Saudi don yin aikin Hajjin shekarar 2022 yayin da 'yan bindiga suka bude musu wuta tare da yin awon gaba dasu na tsawon awanni.

Haka zalika a wata takarda, kwamishinan yada labarai, Isah Bajini Galadanchi, ya bayyana yadda wasu da ake zargin 'yan bindiga ne da ke cin karensu ba babbaka tsakanin yankin kudancin jihar sukayi awon gaba da maniyyatan hajjin da 'yan uwansu da suka yi musu rakiya zuwa sansanin mahajjatan da jami'an tsaron da suka rakasu gaba daya.

"An gano yadda dukkan maniyyatan hajjin suka isa Sakkwoto, babban birnin jihar cikin koshin lafiya bayan jami'an tsaro sun cetosu."
"Yanzu haka jami'an gwamnati sun tarbi dakarun sannan ana kokarin ganin sun yi tafiyar zuwa kasa mai tsarki," a cewar Galadanchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

A wani labari na daban, wani labari mara dadi ya zo mana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta ga wasu Bayin Allah da suke shirin zuwa sauke faralin aikin hajji a kasa mai tsarki.

Jaridar 21st Century Chronicle ta rahoto cewa wannan lamari ya auku a ranar Litinin, a lokacin da maniyyatan suke hanyarsu ta zuwa filin tashin jirgin sama.

A safiyar Talatar nan, 21 ga watan Yuni 2022 ake sa ran cewa maniyyatan jihar Sokoto za su tashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel