Zaben Gwamna 2027: INEC ta Fitar da Sunayen ’Yan Takarar Gwamna 17 a Kano, an Samu Matsala

Zaben Gwamna 2027: INEC ta Fitar da Sunayen ’Yan Takarar Gwamna 17 a Kano, an Samu Matsala

  • Hukumar INEC ta fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar Kano na zaɓen 2027, inda jam’iyyun siyasa 17 suka gabatar da ’yan takara
  • Yusuf Abba Kabir na APC, Abacha Muhammed Sani na PDP da Ibrahim Ali Amin na ADC na cikin ’yan takarar da aka amince da su
  • Abdullahi Mustapha na NDP, mai shekaru 41, shi ne mafi ƙarancin shekaru, yayin da Yusuf Abba Kabir na APC, mai shekaru 63, shi ne mafi girma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar da ta amince da su domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Kano na shekarar 2027.

Jerin sunayen, wanda sakatariyar hukumar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, ya ƙunshi sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu, tare da shekarunsu, jinsinsu da cancantar karatunsu.

Shekarun ’yan takarar gwamnan sun kama daga 41 zuwa 63.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna 2027: INEC ta fitar da sunayen ’yan takara 16 a Gombe, babu Pantami a ciki

An fitar da sunan 'yan takarar gwamna a Kano
'Yan takarar gwamna a Kano | Hoto: Muhammad Abacha| Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

APC, PDP, ADC da sauran jam’iyyu sun tsayar da ’yan takara

Jam’iyyar APC ta tsayar da Yusuf Abba Kabir, mai shekaru 63, a matsayin ɗan takararta na gwamna, yayin da Garo Murtala Sule, mai shekaru 48, zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi.

Jam’iyyar PDP ta tsayar da Abacha Muhammed Sani, mai shekaru 59, tare da Kibiya Yusuf Ado, mai shekaru 68, a matsayin mataimakinsa.

A jam’iyyar ADC kuwa, Ibrahim Ali Amin, mai shekaru 62, ne ɗan takara, yayin da Shehu Abdulkadir Bari, mai shekaru 35, zai yi takarar mataimakin gwamna.

Jerin 'yan takarar Kano a zaben gwamna 2027

Jam’iyyar LP ta tsayar da Santuraki Hamisu, mai shekaru 52, tare da Ibrahim Abbas, mai shekaru 60.

  1. A: Gashash Mukhtar, mai shekaru 56 (Mohammed Safiyanu, mai shekaru 54).
  2. AA: Haruna Abdullahi, mai shekaru 52 (Ismail Abdulmajin Nuhu, mai shekaru 38).
  3. AAC: Sharif Abba, mai shekaru 52 (Idris Uzairu, mai shekaru 46).
  4. ADC: Ibrahim Ali Amin, mai shekaru 62 (Shehu Abdulkadir Bari, mai shekaru 35).
  5. ADP: Muhammad Abdullahi, mai shekaru 48 (Mainika Rabiu, mai shekaru 62).
  6. APC: Yusuf Abba Kabir, mai shekaru 63 (Garo Murtala Sule, mai shekaru 48).
  7. APGA: Tijjani Sukairaju Tijjani, mai shekaru 47 (Auwalu Ismail Yahaya, mai shekaru 53).
  8. APM: Muhammad Bashir Galadanchi, mai shekaru 47 (Umar Abdullahi, mai shekaru 57).
  9. APP: Tukur Aliyu Malam, mai shekaru 54 (Muhammad Ibrahim, mai shekaru 46).
  10. BP: Ahmad Furera, mai shekaru 45 (Muhammad Usman, mai shekaru 40).
  11. DLA: Bari Mustapha Bello, mai shekaru 56 (Musa Abubakar Isyaku, mai shekaru 56).
  12. LP: Santuraki Hamisu, mai shekaru 52 (Ibrahim Abbas, mai shekaru 60).
  13. NDP: Abdullahi Mustapha, mai shekaru 41 (Samira Bala Usman, mai shekaru 40).
  14. PDP: Abacha Muhammed Sani, mai shekaru 59 (Kibiya Yusuf Ado, mai shekaru 68).
  15. PRP: Koguna Nasiru Hassan, mai shekaru 56 (Kabir Abdulhamid Abdulhamid, mai shekaru 45).
  16. SDP: Hussaini Bello Ado, mai shekaru 52 (Garba Lurwan Gaya, mai shekaru 45).
  17. ZLP: Nuhu Isa, mai shekaru 60 (Rabi’u Ibrahim, mai shekaru 54).

Kara karanta wannan

Bayan murabus a gwamnatin Tinubu, INEC ta saka sunan tsohon minista ya yi takara

NDC ba ta cikin jerin sunayen ’yan takarar Kano

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ba ta bayyana a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Kano da INEC ta fitar ba.

A wani rahoto da Legit.ng ta wallafa a baya, hukumar INEC ta cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda aka bayyana a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a Kano, daga cikin jerin sunayen ’yan takarar da ta fitar a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng