Gwamna Ya Fadi Abin da APC Za Ta Tallata Tinubu da Shi domin Saukin Cin Zaɓe

Gwamna Ya Fadi Abin da APC Za Ta Tallata Tinubu da Shi domin Saukin Cin Zaɓe

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana abubuwan ci gaba da Bola Tinubu ya kawo a Najeriya
  • Uzodinma ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin Bola Tinubu su ne babban abin yakin neman zaben APC na wa'adi na biyu
  • Gwamnan ya bayyana cewa Imo ta zama kamar jam'iyya guda, yana mai cewa manufofin Tinubu sun kara kudaden jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya yaba wa Bola Tinubu gMe da ayyukan raya kasa a Najeriya.

Uzodinma ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara yakin neman wa'adi na biyu tun daga ranar da ya hau mulki.

Gwamna ya yabawa salon mulkin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Hope Uzodinma. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Hope Uzodinma.
Source: Twitter

Uzodimma ya bayyana haka ne a Owerri yayin liyafar da aka shirya wa mambobin kungiyar Renewed Hope Ambassadors, cewar The Nation.

Gwamna ya yabawa salon mulkin Tinubu

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun shirya zuwa wurin Bola Tinubu kan tikitin musulmi da musulmi a zaben 2027

Gwamna Uzodinma ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da manufofinsa sun fara haifar da sakamako mai anfani.

Tawagar ta kai ziyara domin duba ayyukan gwamnatin tarayya da na gwamnatin Imo, ya ce nasarorin gwamnatin Tinubu sun zama babban sakon yakin neman zaben APC.

A cewarsa, abin da ke jawo kuri'u shi ne kyakkyawan aiki, ba tarukan yakin neman zabe kadai ba.

Gwamnan ya kwatanta halin da Najeriya ke ciki da tafiyar Bani Isra'ila daga Masar zuwa Kasar Alkawari, yaa ce manyan gyare-gyare kan fuskanci adawa kafin jama'a su fara ganin amfaninsu.

Uzodimma ya ce yakin neman zabe shi ne sa mutane su amince da hangen nesa na shugaba, cewar Daily Post.

Ya kara da cewa miliyoyin 'yan APC, masu cin gajiyar bashin dalibai da shirye-shiryen jin kai suna nuna goyon bayan gwamnati.

Ya bayyana cewa Imo ta zama kamar jam'iyya guda, yana mai cewa akalla mutum 50 masu goyon bayan shirin Renewed Hope suna kowane rumfar zabe. Ya ce hakan zai taimaka wa APC samun nasara.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya fara shirin samawa Tinubu kuri'a miliyan 1 a 2027

An samu abubuwan da za a tallata Tinubu da su domin nasarar zaben 2027
Shugaban kasa, Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Dalilin samun ci gaba a Imo - Uzodinma

Gwamnan ya danganta ci gaban Imo da karin kudaden da jihohi suka samu bayan cire tallafin man fetur. Ya tuna cewa lokacin da ya karbi mulki, saura Naira miliyan 100 kacal bayan biyan albashi.

Ya ce bayan Tinubu ya hau mulki, rabon kudaden FAAC ya karu sosai, inda Imo ta samu sama da Naira biliyan 10. Ya ce wannan ne ya ba gwamnati damar gudanar da manyan ayyuka.

Uzodimma ya ce tun farko ya goyi bayan cire tallafin man fetur saboda ya fahimci cewa hakan zai kara wa jihohi kudaden gudanar da ayyukan raya kasa.

Gwamnan ya ce kudaden shiga na cikin gida sun tashi daga kasa da Naira miliyan 400 a wata zuwa kusan Naira biliyan 3. Ya kuma ce basussukan jihar sun ragu daga sama da Naira biliyan 280 zuwa kasa da Naira biliyan 90.

An karrama gwamnan Najeriya a Amurka

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Bala Adamu ya amince ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027

An ji cewa Majalisar Wakilai ta Amurka ta karrama Gwamna Hope Uzodimma da lambar yabo saboda kyakkyawan shugabancin da yake yi a Imo.

Wannan karramawa na zuwa ne yayin da Gwamna Uzodinma ke shirin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dattawan Birtaniya.

Majalisar ta yaba da ayyukan da gwamnan Imo ya aiwatar a fannin ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.