Daukan ma’aikata 774,000: Keyamo ya sake caccakar majalisa duk da hakurin da babban minista ya bayar

Daukan ma’aikata 774,000: Keyamo ya sake caccakar majalisa duk da hakurin da babban minista ya bayar

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, ya ce mambobin majalisar tarayya na kokarin bi ta kansa wajen daukar ma’aikata 774,000.

Hukumar dibar ma’aikata ta kasa za ta kwashi ma’aikata 774,000 a karkashin shirin ayyuka na musamman.

Karamin ministan ya yi musayar yawu da wasu yan majalisar tarayyar lokacin da ya gurfana a gabansu kan tsarin diban ma’aikata a makon da ya gabata.

Biyo bayan haka, yan majalisar suka dakatar da tsarin dibar ma’aikatan amma Keyamo ya ce basu da wannan karfin ikon.

A wani taro a ranar Talata, Chris Ngige, babban ministan kwadago ya ba shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan hakuri a kan zafin kai da Keyamo ya nuna. Shima Keyamo ya halarci zaman.

Daukan ma’aikata 774,000: Keyamo ya sake caccakar majalisa duk da hakurin da babban minista ya bayar
Daukan ma’aikata 774,000: Keyamo ya sake caccakar majalisa duk da hakurin da babban minista ya bayar Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da yake martani, Lawan ya ce ma’aikatar kwadago za ta samu goyon bayan bangaren dokoki idan har aka bi tsari.

Daga nan sai kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin karkashin jagorancin Godiya Akwashiki, sanata mai wakiltan Nasarawa ta arewa, suka umurci hukumar NDE da ta gabatar da tsarin aiki kan aiwatar da shirin.

Kwamitin ya bukaci hukumar da ta gabatar da tsarin a ranar Litinin.

Amma da yake magana da manema labarai bayan barin taron, karamin ministan ya ce zai koma wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari don jin umurni na gaba.

Ya ce umurnin majalisar dokokin ba zai daure shi ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Magu ya tattara kayansa daga hedkwatar EFCC

“Kun ga cewa dukkanin gwagwarmayar yau kan yadda za a bi ta kaina ne wajen aiwatar da wannan shiri kuma na tabbata duk kun ga hakan,” in ji lauyan.

“Yanzu da tanadin doka, ban san ta yadda za su yi hakan ba, dole ne na koma ga ubangidana wanda shine Shugaban kasar Najeriya domin ya bani umurni.

“Da sashi 3 na dokar NDE, nine shugaban hukumar. Minista ne shugaban NDE. Idan aka ce a koma a kawo wani tsari, dole wurina za a dawo.

"Abu na biyu idan ka duba sashi na 15 na dokar NDE, ya ce minista na iya bayar da dokar bai daya ga NDE. Hakan na nufin, ba za a iya samun tsarin aiki ba, ba tare da ka dawo wajen ministan ba.

“Abu na uku shine cewa nada ni a matsayin minista, shugaban kasar ya bayar da umurni a watan Oktobar shekarar da ya gabata cewa naje na kula da ayyukan NDE gaba daya. Ban ga ta yadda za ka kula da hukuma ba sannan su je su aiwatar da aiki ba tare da amincewarka ba, dole takardun su tsaya a wani teburi.

“Abu na hudu, shine umurnin bai daya da shugaban kasar ya bayar, musamman shugaban kasar ya umurce ni ta wasika a watan Mayun wannan shekara cewa na je na kula da yadda za a aiwatar da wannan aiki. Ta yaya za ka kula da aiki ba tare da umurnin karshe ya fito daga gareka ba. Wannan yardar ya ta’allaka a kan teburina ne.

“Zan kuma koma ga shugaban kasar domin samun umurni. Umurnin majalisar dokoki ba za su yi tasiri ba a kaina.”

Ministan ya ce a karshe, ya zama dole Abubakar Malami, Atoni-Janar na tarayya ya fassara dokoki a karkashin jayayyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel